BABBAN LABARI: Taron Sulhu: Atiku Ya Gabatarwa Buhari Wasu Muhimman Bukatu 5

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP da ya sha kaye a zaben 2019, Atiku Abubakar ya gabbatar da wasu muhimman bukatu 5 da ya ke so daga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya gabatar da bukatun ne a yayin ganawarsa da wata tawaga daga kwamitin zaman lafiya na kasa (NPC) karkashin jagorancin Janar Abdulsalami Abubakar (mai murabus) kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Hausa Dailypost ta gano cewa Atiku Abubakar ya yi gargadin cewa hankulan mutane yana tashi a halin yanzu a yayin ganawarsa da Abdulsami tare da abokin takararsa Peter Obi da sauran jiga-jigan jam'iyyar PDP.
Ga dai bukatun da ya gabatar kamar yadda aka ruwaito.
1. A bude dukkan asusun ajiyar banki na 'yan jam'iyyar hamayya da aka rufe.
2. A daina tura sojoji wuraren zaben da za a gudanar a nan gaba.
3. A rika tantance masu zabe kafin a fara kada kuri'u a sauran zabukan da su kayi saura.
4. INEC ta bude shafinta na Intanet ta yadda dukkan jam'iyyun siyasar da ke takara za su iya shiga su duba yadda abubuwa ke gudana.
5. A saki dukkan 'yan siyasar da ake tsare da su ba bisa kan ka'ida ba.
Atiku ya kuma ce zaben ranar 23 ga watan Fabrairu itace zabe mafi muni tun bayan da Najeriya ta koma mulkin demokradiya inda ya ce an tafka magudi kuma ba a bawa al'umma abinda suke so ba.
Ya lissafa matsalolin da suka faru a zabe kamar haka:-
1. Tura sojoji wurin zabe wanda ya sabawa kundin tsarin mulki da umurnin kotun koli.
2. Tafka magudi da INEC da jam'iyyar APC da dakarun soji suka hada kai suka yi.
3. Kulla makirci tsakanin gwamnatin tarayya da INEC domin kawo cikas ga zabe.
4. Kura-kuren da aka tafka a zaben ya nuna cewa ba bu wata cigaba da aka samu bayan zaben 2015.
An ruwaito cewa Abdulsalami da tawagarsa sun ziyarci Atiku ne domin tabbatar da cewa babu wata matsala da za ta kunno kai a kasar.
Ana sa ran NPC za ta gana da shugaba Buhari domin ta gabatar masa da bukatun Atiku.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "BABBAN LABARI: Taron Sulhu: Atiku Ya Gabatarwa Buhari Wasu Muhimman Bukatu 5"

Post a Comment