Ghana: Hukumar zabe ta rufe shafin ta na internet

Rahotani daga Ghana na cewa an rufe shafin
intanet na hukumar zabe da kasar, yayin da ya
rage kusan makonni biyar a yi babban zaben
kasar.
Da farko dai wasu sun dauka cewa ko masu
satar shiga shafukan intanet ne suka shiga
shafin, sai dai hukumar ta ce na'urar intanet din
ce ta samu matsala kuma ana kokarin gyarawa.
Wasu 'yan kasar dai na ganin cewa akwai lauje
cikin nadi kan wannan hukunci da hukumar zabe
ta dauka.
A baya dai duk wasu bayanai da ake bukata da
suka shafi shirye-shiryen zaben da ma lokutan
zaben a shafin na hukumar zabe ake samu.
Dan haka sun yi kira da a dauki matakin gaggawa
na gyara shafin internet din na hukumar zaben
Ghana, dan saukakawa jama'a sanin halin da ake
ciki a kasar.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

Related Posts :

0 Response to "Ghana: Hukumar zabe ta rufe shafin ta na internet"

Post a Comment