GOOGLE ALLO SABON CHATTING DA YAFI WATSAPP
dan ba'a manta ba, kamfanin google a kwanakin baya sun fitar da wani application mai suna Google Duo wanda yake zama wata kafa ta sadarwar hoton video (video chat).
Google sun kara fitar da sanarwar cewa sabon chatting app dinsu da suka yiwa lakabi da google allo na nan zuwa nan bada jimawa ba, inda zaizo da sabbin abubuwa da mafi yawa daga cikin chatting apps basu dasu.
Google dai kamar sauran chatting apps yana da features na tura sakon text , hotuna , hotunan yanayi (emojis) , videos , sautin murya da sauran sautuka, files dadai sauran makamantan abubuwan da sauran chatting apps ka iya.
Nasan a haka wasu zasu ce ai babu bambanci tsakaninshi da sauran apps tunda duk a cikin abubuwan da na.zayyano a sama babu wani bakon abu. To kwantar da hankalinka in bayyana maka abinda ya bambance shi daga sauran chatting apps.
Ba kamar sauran apps ba, google allo yana dauke da google search a cikinsa wanda zaka yi ba tare da ka bar cikin app din ba. Sannan kuma akwai search na murya(voice search) a yayin da kake jin gandar yin rubutu. Haka zalika app din na dauke da tsarin auto reply da zai kawo maka reply da yake tsammani a zuciyarka wanda kai kuma zaka bashi damar tunawa in yayi daidai da abinda kake so.
Dadin dadawa, google allo zaizo da tsari da zai baka damar tattaunawa da google bot yayin da kake chat wanda hakan zai kara baka damar more wasu karin abubuwan.
Ya zuwa yanzu dai shi wannan sabon application bai iso ba tukun amma zaka iya zuwa playstore kai search dinshi domin kayi pre-register da zai sanar da kai da zarar an saki wannan application din.
0 Response to "GOOGLE ALLO SABON CHATTING DA YAFI WATSAPP"
Post a Comment