Trump zai ci gaba da shirin inshorar lafiya na Obama

Zababben shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa zai ci gaba da tafiyar da shirin Shugaba Obama na inshorar lafiya.
Soke shirin inshorar lafiyar da ake yi wa lakabi da Obamacare na gaba-gaba cikin jerin abubuwan da Donald Trump ya yi ta nanata cewa zai yi a lokacin yakin neman zabe, yana mai cewa shirin tamkar wani babban bala'i ne ga kasar.
Su ma wasu shugabannin jam'iyyar Republican sun bayyana a babban taron jam'iyyar cewa tsarin inshorar lafiyar tamkar katsalandan ne da gwamnati ke yi a harkar kiwon lafiya.
Sai dai yanzu a wata hira da ya yi da mujallar Wall Street Journal, zababben shugaban kasar ya nuna cewa zai iya ci gaba da aiwatar da wasu muhimman abubuwa da ke kunshe a shirin inshorar lafiyar wadanda ya ce yana matukar so.
Tun bayan nasararwar da aka yi ta yin nasararsa a zaben da aka yi ranar Talatar da ta wuce, Mista Trump yake ta sanar da sauye-sauye kan alkawuran da ya yi a lokacin yakin neman zabensa.
Ya zuwa yanzu dai ya sauya fasalin mambobin kwamitinsa na karbar mulki inda ya ragewa gwamnan New Jersey Chris Christie mukami, sannan ya nada zababben mataimakin shugaban kasa Mike Pence a matsayin mai sanya ido a kan nada jami'ai 4,000 kafin rantsar da shi a ranar 20 ga watan Janairu.
Akwai kuma wasu mukamai da aka ware ga manyan 'ya'yan Mr Trump din su uku da kuma wasu da ke tsayawa kusa da shi a lokutan yakin neman zabe da suka hada da tsohon magajin garin New York Rudy Giuliani da tsohon kakakin Majalisar wakilai Newt Gingrich.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Trump zai ci gaba da shirin inshorar lafiya na Obama"

Post a Comment