Lampard zai bar buga-leda a New York City

Tsohon dan kwallon Chelsea, Frank Lampard, ya
ce zai bar taka-leda a kungiyar New York City
wadda take buga gasar Amurka.
Lampard mai shekara 38, wanda yarjejenirsa za
ta kare a kungiyar a karshen shekarar nan, ya
rubuta a shafinsa na sada zumunt na Instagram
cewa lokacin da zai bar kungiyar ya yi.
Dan wasan ya ce a nan gaba kadan zai sanar da
sabuwar kungiyar da zai koma da taka-leda.
Lampard ya ci kwallaye 15 a wasanni 31 da ya
buga wa New York a shekara biyu da ya yi, ya
kuma buga wasanni aro a Manchester City.
Dan wasan ya bar Chelsea a shekarar 2014 a
matsayin wanda ya fi ci wa kungiyar kwallaye a
tarihi, inda ya ci guda 211.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Lampard zai bar buga-leda a New York City"

Post a Comment