Zaben Trump ya jawo samun karuwar tallafin zubar da ciki

An samu karuwar bayar da taimako ga daya
daga cikin manyan kungiyoyin da ke taimakawa
wurin zubar da ciki, Planned Parenthood,
sakamakon zaben Donald Trump da
mataimakinsa.
Ana aika tallafin ne da sunan mataimakin Trump
din Mike Pence wanda yake matukar adawa da
zubar da ciki, a matsayin wani shagube domin
kunyata shi.
Za a aika wa Mista Pence takardar shedar duk
taimakon da aka bayar ga kungiyar ta Planned
Parenthood, da sunansa.
A lokacin da yake dan majalisar wakilan Amurka
na Indiana, kuma daga bisani ya zama gwamnan
jihar, Mista Pence ya bullo da tsauraran matakan
hana zubar da ciki a Amurka.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Zaben Trump ya jawo samun karuwar tallafin zubar da ciki"

Post a Comment