KANNYWOOD: Manyan Fina Finai Guda 7 Wanda Zasu Fito Ranar Sallah

Manya manyan furodusosin masana’antar shirya fina finai ta Kannywood sun shirya fito da wasu daga cikin fina finan da aka dade ana tsumayi a lokacin shagulgulan sallah karama.
Rahama Sadau za ta fitar da fim din ta mai suna Rariya wanda Yasin Auwal ya bada umarni a ranar 26 ga watan nan.
Fim din Ali Nuhu Mansoor shi ma ana tsammanin zai fito a daidai lokacin da ake bukukuwan Sallar.
haka zalika na Abubakar Mai Shadda Kanwar Duba rudu , wanda Ali Nuhu da Rahama Sadau suka fito a matsayin ya da kanwa.
Sai kuma fin din Zaharaddeen Sani
Abu Hassan wanda ya bada labarin tabargazar da wata kungiyar ta’addanci ta yi a gari kafin a karshe sojoji su murkushe ta.
Sauran da ake tsammani za su fito a lokacin sun hada da
Bintoto, Sultana da Munaqisa
An dai dakatar da fitowar fina finan saboda zagayowar watan Ramadan.
Wannan shi ne karon farko a masana’antar da za a haska manyan fina finai irin wadannan a lokaci daya a sinima.

YOU MAY ALSO WATCH THIS 
DADIN KOWA EPISODE 11

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "KANNYWOOD: Manyan Fina Finai Guda 7 Wanda Zasu Fito Ranar Sallah"

Post a Comment