Kannywood: Yadda Maryam Yahaya (Mansoor) Ta Girgiza Kannywood

Ga duk mai bibiyar harkokin masana’antar shirya finafinan Hausa watau Kannywood, ya kwana da sanin bullar sabuwar jaruma Maryam Yahaya (Mansoor), wadda za a iya cewa ta shigo farfajiyar fim da kafar dama, kasancewar ta zamo cikin jerin taurarun da ake sa ran za su haska nan da shekaru masu zuwa.
Akwai mamaki matuka yadda cikin lokaci kankani jarumar ta yi wa takwarorinta fintikau wajen yawan fitowa a finafinai masu kyawun gaske, ko da yake ba abin mamaki ba ne idan aka yi la’akari da kamfanin FKD Production da ya tsaya tsayin daka wajen yi mata babban fim watau MANSOOR, wanda za a saki a satin karamar Sallah a sinimun da ke fadin kasar nan, ranar 30 ga watan Yuni 2017.
Maryam, ‘yar asalin Jihar Kano, ta shimfida kwarewarta a farfajiyar, gwana ce ta gwanaye, wadda take yin kyau da zarar an dora mata kyamara. Wani karin armashi game da ita shi ne, yadda ba ta wasa da aikinta a matsayin jaruma.
Bajintar da ta nuna a fim din, MANSOOR, duk da cewa ba shi fim na farko da ta fara fitowa ba, amma an ga yadda tauraruwarta ta haska (wanda aka gani tun kafin fim din ya fita) shi ne ya janyo mata farin jinin tun kafin ya fita. Tallansa kawai jama’a suka gani, amma suka tabbatar da cewar Maryam Yahaya za ta yi abun kirki a masana’antar fim.
Tun daga nan manyan furodusoshi suka fara nuna ra’ayinsu na sanya ta a finafinansu, kafin ka ce kwabo jarumar ta kai matsayin da take a yau, na zamowa cikin jerin manyan jaruman da Kannywood ke alfahari da su.
Cikin shekara daya kacal da fara yin fim, jarumar ta zamo tauraruwar da kowane lungu da sako ake labarinta. Gwana ce wajen iya aktin, musamman da ta kasance tana iya taka kowace irin rawa da aka dora ta matukar ba za a wuce gona da iri ba.
Masana’antar Kannywood ta dade ba ta samu jaruma da cikin lokacin kankani ta shige sahun takwarorinta ba, domin an saba ganin yadda wasu jaruman ke daukar shekaru kafin ‘yan kallo su gamsu cewar kwararru ne, balle har manyan furodusoshi su rika aiki da su a kai a kai.
Sai dai masana na ganin tagomashin da ta samu na horo daga wurin maigidanta jarumi Ali Nuhu, shi ne ummul’aba’isin kasancewarta kwararriya a masana’antar Kannywood.
Babban abin da yake kara mata farin jinni tsakanin abokan sana’arta shi ne girmama na gaba, karamci, mutunci da sanin girma mutane.
Har ila yau, jarumar ta dan yi tsokaci kadan game da abubuwan da ta fuskanta daga gida kafin a amince mata ta fara harkar fim.
“Dole ne duk wanda ya samu kansa a wannan hali zai iya samun matsala, musamman a gidansu za a ji irin ba dadi din nan. Amma daga karshe ina nuna masu harkar fim sana’a ce tamkar kowane irin aiki, lokacin da kake bakin aiki magana a waya ma jarumi ba shi da damar yi balle ya samu damar zuwa yawo.
“Kuma ina son mutane su sani, fim sana’a ce kuma ko wace masana’anta akwai nagari akwai kuma na banza. Idan ka tsare kanka Allah Zai taimake ka, saboda kai dai ka san me ka je yi, idan ka je iskanci ne kai ka sani, idan ma ka je a wulakance ne kai ka sani idan kuma ka je da mutuncinka Allah zai kare maka mutuncinka.” A cewar Maryam.
Jaruma Maryam Yahaya ta ciri tuta, ta kafa tarihi a masana’antar Kannywood, ta zamo gwana da ta ta yi bajintar a zo a gani cikin kankanin lokaci, alamu sun nuna matukar jarumar ta dage kan kadamin da ta taho a kai, babu shakka nan da wani lokaci za ta shiga sahun manyan jarumai mata da duniyar fim ke labari.
Cikar jaruma shi ne yin abin da darakta yake so, a lokacin da yake so. Haka zalika rawar da jaruma kan taka fim kan zamo wani siradi na sirrin nasararta. Batun kyau da cikar zati kuwa na karawa jaruma kwarjini a idanun ‘yan kallo, ta yadda idan ba jarumar da suke so suka gani a fim ba, bai cika birge su ba.
Finafinan da ta fito ciki sun hada da: Tabo, Mijin Yarinya, ‘Yar Main Ganye, Duhun So, da Arashi.
Ta samu magoya baya da yawa a shafukan sada zumunta, musamman Instagram, inda take amfani da @MaryamYahya.

WATCH THIS


SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Kannywood: Yadda Maryam Yahaya (Mansoor) Ta Girgiza Kannywood"

Post a Comment