Nafi Buhari Bawa ‘yan Nigeria ‘yanci — Inji Tsohon Shugaban Kasa Jonathan
Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya mayar da martani ga yunkurin gwamnatin kasar na yin dokar da ta haramta furta kalaman nuna kiyayya tsakanin al’ummomin kasar.
Mista Jonathan ya sake wallafa wani hoto a shafinsa na Facebook wanda ya yake dauke da rubutu kamar haka:
“Ni ne shugaban da aka fi zagi da suka a duniya, amma za a tuna da ni idan na bar mulki saboda cikakken ‘yancin da gwamnatina ta bai wa jama’a,” kamar yadda sakon ya ce.
Ya wallafa wannan sakon ne a shafin ranar Alhamis bayan wallafawar farko a watan Disambar shekarar shekarar 2014.
A makon jiya ne Mataimakin Shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo, ya ce gwamnati za ta fara daukar amfani da kalaman nuna kiyayya a matsayin ta’addanci.
Hakazalika a jawabin da Shugaba Buhari ya yi wa al’ummar kasar ranar Litinin, ya tabo batun yadda wasu suke kalaman da suke ketara ikokin dokokin kasar a kafofin sada zumunta.
Abin da ya sa wasu ‘yan kasar suke ganin wata kila gwamnati ba ta jin dadin yadda jama’a suke sukarta musamman a kafofin sadarwa na zamani.
A ranar 12 ga watan Agustan nan ne gwamnatin Najeriyar ta ce ta fara shirye-shiryen aike wa da wata bukata zuwa ga majalisar dokokin kasar da ke neman yin dokar da za ta fayyace irin hukuncin da za a yi kan wadanda aka samu suna furta kalaman kiyayya ga wani jinsi a kasar.
Gwamnati ta yanke shawarar yin hakan ne saboda yadda zaman tankiya ke karuwa tsakanin a kabilu da addinai da kuma yankunan kasar daban-daban, inda har wasu ke kiran da a raba ta ko a sake mata fasali.
0 Response to "Nafi Buhari Bawa ‘yan Nigeria ‘yanci — Inji Tsohon Shugaban Kasa Jonathan"
Post a Comment