Dalilin Da Ya Sa Nake Boye Wasu Abubuwan Da Suka Shafe Ni – Nafisa Abdullahi

A wannan ‘yar gejeriyar tattaunawa da aka yi
da shahararriyar jarumar Kannywood Nafisa
Abdullahi, jarumar ta tabo batun halin da
masana’antar fim take ciki, har ila yau ta dan
yi albishir ga masoyanta kan sabon shirinta.
Kwana biyu an ji ki shiru a finafinai, ko akwai
wani abu a kasa ne?
To, gaskiya ba zan ce an ji shiru ba, kawai da
hutu ne kamar yadda kowa yake yi.
Kuma na yi hakan ne domin na mayar da
hankali kan sabon fim dina da yanzu haka
muke shiryawa, yana nan fitowa nan ba da
jimawa ba.
Duk inda jarumi ko mai shirya fim yake, akwai
bukatar ya rika nutsuwa domin yin nazarin
abu mai kyau.
Fim ba don tsirarun mutane ake yi ba, ana yi
ne saboda al’umma da yawa. Saboda haka,
dole ana bukatar yin tunanin na kwarai ta
yadda za a zo wa da mutane abun da za su yi
saurin karba.
Finafinai nawa ne aka sa kike yi yanzu?
Ina da finafinai da yawa wadanda aka kawo
min labarinsu.
Ba lallai in ce Eh ko A’a ba, tun da komai
yana tafiya ne bisa tsari.
Ba komai ne zan bayyana ba dalla-dalla a
halin da ake ciki yanzu ba.
Albishin din da zan yi wa masu kallon finafinai
Hausa shi ne, sabon shirin da muke kokarin
zuwa da shi, hakika zai kayatat matuka da
gaske.
Na yi maganar finafinai da yawa, amma ba
kowane ne aka cimma matsaya ba. Zamowa
wadda mutane ke so ba yana nufin kowane
fim sai na fito a ciki.
Hutun da na tafi yana da alaka da sabon
tunanin da nake son zuwa da shi a wannan
masana’anta. Shi fim, kamar yadda aka sani,
hanya ce ta isar da sako ta hanyar nishadi,
saboda haka lallai ka zo da sakon da zai
burge mutane.
Ko za ki iya shaidawa mutane sunan fim din?
To, yanzu dai mun rada masa suna KARMA.
Shin kun kusan kammala shi wannan shirin
ne?
Zuwa yanzu zan iya cewa mun kammala
kusan kaso 70 cikin 100. Amma ka san yanzu
abubuwa sun canja, saboda haka muna da
sabbin hanyoyi da muka bullo da su na tallata
wannan fim da zai dace da yadda ake yi a
fadin duniya.
Mun ajiye tunanin kasuwanci fim da gama-
gari. Wannan karo sabbin tsare-tsare ne da
muke sa ran haska fim din a wasu kasashe,
ba wai Nijeriya kawai ba.
Yaushe za a saki fim din?
Ba zan fadi wannan ba a halin yanzu ba. Abin
da na sani shi ne muna aiki tukuru don
tabbatar da ganin mun kayatar da mutane.
Lokaci ne kawai zai bada damar haka. Idan
lokaci ya yi kowa zai ji labari.
Ko za ki dan yi tsokaci game da abin da fim
din ya kunsa?
Ba yanzu ba tukun. Ina da dalilaina ba boye
wasu abubuwan da suka shafi lamari irin
wannan kafin a kammala. A wasu lokutan,
idan ka bayyana abu, a karon farko sai ka ga
ka ragewa mutane karsashi.
Amma ina tabbatarwa da masu kallon
finafinan Hausa cewar, Nafisa Abdullahi da
aka saba gani, to a cikin wannan shiri ta
canja, domin za ta bayyana ne a wata siffa
daban.
Shi ya sa nake ta fadi tunanin da muka yi ya
ba mu damar kirkiro abubuwa da yawa. Duk
lokacin da ka samu nutsuwar yin tunani, to
babu shakka za a zo da abu mai kayatarwa.
Fim dina da zai fito nan gaba, rawar da na
taka mutane ba su taba gani na a cikinta ba.
Ni ce dai, amma masu kallo za su ce, tabbas
mun ga sabon abu

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Dalilin Da Ya Sa Nake Boye Wasu Abubuwan Da Suka Shafe Ni – Nafisa Abdullahi"

Post a Comment