ALJANINE AJIKINKI
👻 *ALJANI NE A JIKIN KI //5* 👻
*GUDUNMUWAR DA ZAN IYA BAKU NA MAGANI DA ADDU'OI*
Kamar yanda na fada a farko cewa dalilin yin taqaitaccen rubutun nan shine saboda yawan tambayoyi da muke samu akan matsalolin mata wanda aljanu ne amma sun kasa fahimtar haka. Rubutun don in kin san kina da aljani ne kije ki nemi magani amma ba wai ki nema a social media ba. Ban san komai game da bada maganin aljani ba, don wasu suna ta tambayar magani, ko likita ne baya bada magani a social media zai ce kije asibiti ne, saboda wata kila akwai abun da ido da ido ne zai fahimta, don haka a nemi magani na zahiri, ba wai ayi ta boye ciwo ana tambaya a nan ba.
Amma dai zan bada abin da na bawa mutane da dama kuma sun ga amfanin sa, shima din wani mai ruqya ne ya taba fada mun, sannan zan qara muku da addu'oi, gasu kamar haka:
1.Habbatus sauda na gari
2. Habbatus sauda oil
3. Musk ja
4. Garlic oil
5. Zaitun
Zaki mayar da garin habbatus sauda kamar komai naki, kullum ki cire kayan ki duka, sai ki samu abu babba ki lullube, sannan ki zuba garin Habbatus sauda, har sai hayakin ya kare tsaf a jikinki.
Sannan idan zaki yi wanka ki debi garin dan dai-dai shima ki zuba kiyi wanka dashi.
Idan zaki ci breakfast ki zuba kadan a tea ko kunu, haka nan a cikin kosai ko egg. Haka ma da rana, ki barbada a cikn abincin ki, haka nan ma a ruwan shan ki, ya zamana kina amfani da habbatus sauda sau hudu kenan.
A abinci, a abin sha, ruwan wanka, hayaki. Ya zamana koda baki ci a ko wane abinci ba, kada ki bari dai gari ya waye har ki yammatu baki yi amfani dashi ba, don ni wani lokacin haka nan ina ďiban garin in saka a baki na, saboda ba tsami, ba bauri, kuma ba wari, sannan ina enjoying shansa a cikin tea, kuma nakan zuba shi a cikin abin da nake yawaita ci ko sha haka, yanda mutum ba zai manta ba. Habbatus sauda magani ne ko kina da matsala ko baki dashi, wasu har a abinci suna hadashi a cikin spices.
Sannan zaki iya sawa a cikin man kitson ki, ko garin ko oil duk wanda ya samu a rinka miki kitso dashi.
Bayan nan, sai ki hada zaitun, habbatus sauda, da kuma man tafarnuwa, ki rinka shan rabin tea spoon safe da yamma, dan kadan in dai ya shiga cikin ki shikenan, shima magani ne sosai, kuma yana gyarawa mace hailarta, yana hana ciwon cikin during menstruation, yana saukarwa mace da ni'ima kuma yana kashe infection in kina dashi. Sannan idan kin gama jini kafin kiyi tsarki ki shafa shi a farin auduga wato musk kenan ki saka a gabanki.
Kuma zaki lakata habbatus sauda a hancinki kija ya shiga kanki zaki ji shi har maqoshinki, shima yana hana aljani zama jikin mutum.
Shi kuma musk din, abin da zaki yi dashi shine, zaki lakato da abun goge kunni, saboda a daskare yake, ki shafa a gaban kumban ki, wato in da kike sa reza kike yankewa a duka yatsun ashirin, kafa da hannu kenan.
Sannan ki shafa a gaban ki, da anus dinki, da cibiyar ki, da nipples dinki, da kunnuwanki, da hancin ki, da bakin ki, duka hujin jikin ki kenan 32. Wannan shi zaki yi ne kullum in zaki kwanta.
Wainnan ayoyin da surorin su kuma kullum zaki samu lokaci ne ki karanta su duka lokaci daya ban da tsallaken rana, kullum kiyi.
1. Suratul Buruj (Wassama'i zatul buruj) sau 3.
2. Suratul Yasin sau 1.
3. Suratul Mulk.
4. Ayoyi biyun karshen suratul Qalam.
5. Sannan sai Suratul Mu'minun aya ta 97 da 98, su kuma zaki karanta sama da sau 11.
6. Suratul Furqan Aya ta 23 ki karanta sau ba adadi.
Idan kin yi sati biyu ko uku kina karanta su sai ki koma karanta suratul Buruj sau uku da safe, uku da rana uku da yamma.
Sannan da qoqarin kwanciya da alwala, da kuma yin adduo'in bacci, in kika duba hisnul muslim zaki gansu. In kuma ba zaki iya ba sun miki tsaho to kada ki kwanta ba tare da kin yi wainnan ba, Falaq, Nasi, da Qulhullahu sannan da ayatul kursiyyu da mulk ki shafe jikinki dashi.
Da karanta Falaq nasi suratul Ahad Ayatul Kursiyyu bayan ko wani sallah.
Sannan kuma ki kula da wainnan adduo'in:
أُعِوذ بِكَلِـمَاتِ اللَّهِ التَّـامَّةِ ، مِنْ كُلِّ شَيْـطَانٍ وَهَـامَّةٍ ، وَمِنْ كُـلِّ عَـيْنٍ لَ
0 Response to "ALJANINE AJIKINKI "
Post a Comment