ARBA'UNA HADISI


Kadaure kakaranta zaiyimaka amfani duniyarka da lahiraka.

Markazus salafiyya
07035217923

HADISI NA FARKO
Manzon Allah (S.A.W) ya na cewa Wanda ya karanta Qulhuwallahu Ahad kafa 10x Allah ya yi masa Alkawarin zai gina masa katafaren gida a gidan Aljanna. Sai Sayyidina Umar ya ce Ai to in haka ne sai mu dinga yawaitawa, sai Manzon Allah ya ce Allah shine mai yawaitawa Allah shine mai tsabtacewa.

HADISI NA BIYU
Manzon Allah ya na cewa duk wanda ya karanta suratul Kahfi a ranar jumaa Allah zai cika masa hasken sa har zuwa wata jumaa mai zuwa yana cikin haske yana cikin farin ciki.

HADISI NA UKU
Annabi Muhammad (S.A.W) ya ce duk wanda ya haddace ayoyin goma na farkon kahfi Allah zai kiyaye shi daga fitinar Dujjal.

HADISI NA HUDU
Manzon Allah yana cewa Wanda ya karanta ayatul kursiyu bayan kowace Sallah ta farillah ba abinda zai hana shi shiga Aljanna sai in bai mutu ba.

HADISI NA BIYAR
Idan kazo zaka kwanta a shimfidar ka da daddare to ka karanta kulya ayyu hal kafirun to bazaka mutu mushriki ba  idan ka mutu a wannan daren.

HADISI NA SHIDA
Wanda ya yi alwala, bayan ya kare alwala sai ya ce Ash-hadu alla ilAha illallAh wahadahu lasharika lahu wa anna muhammadan Abduhu wara suluhu. Allahumma Ja'alni minattauwabina waja'alni minal mutadhahhirina.
Duk wanda ya fadi wannan bayan gama Alwalar sa to za'a bude masa kofofin Aljanna guda takwas ya zabi wadda ya ke son shiga.

HADISI NA BAKWAI
Wanda ya yi alwala bayan ya kammala alwalar sa kaf, sai ya ce Subhanakallahumma Wabihamdika ash-hadu allah Ilaha illallah anta astagfiruka wa'atubu ilaika.
Zaa rubuta wannan acikin wata takarda baza'a bude ta ba sai ranar lahira ya ga alkhairin da ke cikin ta.

HADISI NA TAKWAS
Wani Sahabi ya ke cewa wata rana muna tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi wasallama sai wani mutum daga cikin sahabbai ya ce Allahu Akbar kabirah, Walhamdulillahi kasirah, Wasubhanallahi bukratan waasilah, Sai Manzon Allah ya ce wanene cikin ku ke fadar wannan kalma, sai ya ce ni ne Ya rasulullah sai Manzon Allah ya ce nayi mamakin wadan nan kalmomi da ka fada, anbude kofofin sama gaba daya saboda wannan kalma da ka fada.  Sai Abdullahi Dan Umar ya ce tun daga wannan rana kullum sai na fadi wannan kalma, ban taba tsallake wata rana ko wani lokaci da bana fadar wannan kalma ba.

HADISI NA TARA
Wata rana mun kasance muna Sallah a bayan Manzon Allah (S.A.W) da Annabi ya dakko daga ruku'u sai ya ce Sami'Allahu Liman Hamidahu sai wani mutum daga cikin sahabbai yace Rabbana Walakal Hamdu, Handan Kasiran Dayyiban Mubarakan Fihi da aka gama sai Manzon Allah ya waiwayo sai ya ce Wanene ya fadi wannan sai mutumin yace Ni ne ya Manzon Allah sai Manzon Allah ya ce Naga Malaika talatin da "yan kai suna rigagato wazai rubuta wannan aiki yaje ya gayawa Allah.

HADISI NA GOMA
Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce Wanda ya yi sallar nafila rakaa goma sha biyu tsakanin dare da rana Allah zai gina masa gida a cikin gidan Aljanna.

HADISI NA SHADAYA
Wanda ya kiyaye yana yin nafila raka'a hudu kamin sallar azahar da kuma raka'a hudu kamin sallar la'asar to Allah zai haramta masa shiga wuta.

HADISI NA SHA BIYU
Manzon Allah Yana cewa Allah ya jikan wanda ya yi sallar nafila raka'a hudu kamin la'asar.

HADISI NA SHA UKU
Wanda yake karanta ayoyi goma da daddare to baza'a rubuta shi cikin gafalallu ba, wanda ya ke karanta ayoyi dari to za'a rubuta shi cikin masu bauta ga Allah, wanda kuma ke karanta ayoyi dubu a cikin dare kullum to za'a rubuta shi daga cikin masu arzikin lahira.

HADISI NA SHA HUDU
Wanda da yi Sallar nafila a cikin duhu inda bawanda zai ganshi to Allah zai linka masa sau ashirin da biyar na sallar da zai yi wani ya ganshi.

HADISI NA SHA BIYAR
Annabin tsira ya ce Wanda yayi sallar walha (Sallar hantsi/Luha) rakaa hudu kuma yayi rakaa hudu kamin sallar laasar, Allah zai gina masa gida a cikin aljanna.

HADISI NA SHA SHIDA
Hakika malaiku suna yin salati ga wadanda suke cika sahun farko, idan suka ga wata kafa a cikin Sallah suna cikata basa ba

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "ARBA'UNA HADISI "

Post a Comment