RUBUTU NA BIYAR 5 KAN ILIMIN TAJWIDI
✍RUBUTU NA BIYAR (5) KAN ILIMIN TAJWIDI
🔎TAMBAYA:
Menene fa'idan ilimin Tajwidi?
🎙AMSA:
Kiyaye harshe daga yin kuskure cikin Alqaur'ani mai girma.
🔎TAMBAYA:
Menene bagiransa? (Gurin da ake yinsa)
🎙AMSA:
Alqur'ani mai girma, ta yadda halayan bada shi yake.
🔎TAMBAYA:
Menene falalansa?
🎙AMSA:
Yana cikin manyan ilmomin addini saboda alaqansa da haqiqanin yadda ake bada (koyar) da mafi daukakan zantuka (Qur'ani), sannan yana daga cikin abubuwan da aka kebance wannan al'umman da ita.
🔎TAMBAYA:
Wanene ya fara rubuta shi? (ilimin)?
🎙AMSA:
Ma'abota koyar da ilimin wa'yanda suka kafa abin da aka dauko zuwa garesu daga annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. ________________________________________________________
📓LITTAFI:
Albayan Fee Ilmit-Tajweed
🖌MAWALLAFI:
Malam Ibrahim Sarki (Wamaa Yughnee)
📻DAGA DAN UWAN KU:
Uthman Uzairu musa
Via:07035217923
Markazus Salafiyya
0 Response to "RUBUTU NA BIYAR 5 KAN ILIMIN TAJWIDI "
Post a Comment