Wani Yarima ya sha bulala a Saudiyya

Rahotanni sun ce mahukunta a Saudiyya sun
zane wani Yariman gidan sarautar kasar bayan
da aka same shi da aikata laifi.
Wannan na zuwa ne makwanni kadan bayan da
aka kashe wani jinin sarautar kasar bisa laifin
kisan kai.
Amma kawo yanzu ba a bayyana suna ko ainahin
laifin da yariman ya aikata ba.
Sai dai ba kasafai ake samun jinin gidan sarautar
da laifi ba ko kuma a yanke musu irin wannan
hukunci.
Wasu masu amfani da shafukan sada zumunta a
kasar sun yi farin ciki da hukuncin, suna masu
cewa ya nuna yadda shari'ar Musulunci ke bi ta
kan kowa.
Kawo yanzu ba a bayyana wannan labari a
hukumance ba.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Wani Yarima ya sha bulala a Saudiyya"

Post a Comment