Nigeria: Da kyar wasu jama'a ke samun na cin abinci

Wasu magidanta a Najeriya suna ji a jika
sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da
kuma koma bayan tattalin arziki a kasar.
Daga dukkan alamu wannan hali zai kara
tsananta bayan da hukumar kididdiga ta kasar ta
ce an samu karin koma-bayan tattalin arziki da
kashi 2.2 cikin dari a watanni ukun da suka
gabata.
An danganta wannan matsala da rashin isassun
kudaden kasashen waje da kuma hare-haren da
'yan bindiga ke kai wa a yankin Niger Delta mai
arzikin mai.
A kan haka ne wakilinmu a Kano Mukhtar Adamu
Bawa ya ziyarci wani magidanci a gidansa don
ganin yadda suke cin abincin dare.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Nigeria: Da kyar wasu jama'a ke samun na cin abinci"

Post a Comment