Jam'iyyar adawa ta masu ra'ayin gurguzu a Bulgaria ta yi zarra

Sakamakon jin ra'ayin masu zabe a Bulgari ya
nuna cewa jam'iyyar adawa ta masu ra'ayin
gurguzu wanda dan takararta ke son kulla
dangantaka da Rasha ta samu nasara a zagayen
farko na zaben shugaban kasar da aka yi.
Ana kyautata zaton Rumen Radev ya samu kaso
daya bisa hudu na kuri'un da aka kada, inda
hakan ya nuna cewa ya samu nasara a kan
abokiyar takararsa Tsetska Tsacheva ta
jam'iyyar da ke mulki a kasar.
Idan har aka tabbatar da sakamakon zaben, to
hakan ya nuna cewa firayim minista Bokyo
Borisov ya samu koma baya.
A ranar Lahadi mai zuwa ne za a gudanar da
zagaye na biyu na zaben tsakanin manyan 'yan
takara biyu.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

1 Response to "Jam'iyyar adawa ta masu ra'ayin gurguzu a Bulgaria ta yi zarra"