Akalla Mutum Takwas Ne Suka Mutu A Wajen Kallon Kwallo

Mutum takwas ne aka bada rahoton sun mutu bayan ruftawar wata katanga a babban filin wasan kwallon kafa a kasar Senegal.



Ana kuma fargabar karin wasu 49 sun samu raunuka.
Hadarin ya faru ne a babban filin wasan kwallon kafa na Demba Diop da ke Dakar babban birnin kasar ta Senegal, lokacin da ake buga zagayen karshe na gasar cin kofin kalubale tsakanin kungiyar wasan kwallon kafa ta Stade de Mbour and Union Sportive Ouakam.
Kafafen yada labarai da dama sun bada rahoton cewa fada ne ya barke tsakanin magoya bayan kungiyoyin masu fafatawa da juna, inda ‘yan sanda suka mayar da martani da harba hayaki mai sa kwalla, da ya haifar da rudani.
Wani likitan gagggawa da ke aikin ceto, da kuma shugaban hukumar kwallon kafa ta kasar Senegal ne suka tabbatar wa da BBC adadin wadanda lamarin ya rutsa da su.
Har yanzu dai babu wasu bayanai daga hukumomin tsaro.
-LABARAI, BBC HAUSA

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Akalla Mutum Takwas Ne Suka Mutu A Wajen Kallon Kwallo"

Post a Comment