Kannywood: Jarumi Ali Nuhu Ya Saki Zazzafan Fim Dinsa

 ranar Alhamis 29 ga watan Yuni ne Ali Nuhu, wanda aka fi sani da Sarkin Kannywood ya sake baje kolin da gwanintarsa da hazakarsa, inda ya fitar da sabon Fim, Mansoor.
A cewar Ali Nuhu ya kwashe sama da shekaru goma yana tunanin akan fim din Mansoor, sa’annan an kwashe kimanin shekaru biyu ana shirya shi da tsara shi, kuma Mansoor ya lashe kimanin naira miliyan 8 a jimlace.
BBC Hausa ta ruwaito an kaddamar da wannan Fim ne a katafaren gidan Sinima dake jihar Kano, sa’annan daga bisani ne za’a fara sayar da fayayansa na bidiyo.
Ali Nuhu ya shaida ma majiyar HAUSATOP.com cewa jigon labarin Mansoor wani matashi ne da aka same shi ta cikin shege, kuma mahaifiyarsa ta ki yarda ta bayyana masa hakan, har sai da soyayya ta debe shi, inda iyayen budurwarsa suka yi masa gorin Uba.
Daga nan ne fa ya shiga duniya neman mahaifinsa. Ali Nuhu yace muhimmin darasin cikin fim din Mansoor shine kada ka yi ma mutum gori a duk halin da ka tsince shi, sa’annan kada ka tsangwame shi.
Wasu daga cikin jaruman Fim din sun hada da Maryam Yahaya, Umar M Sharif, Baballe Hayatu, Abba El-Mustapha da sauransu.

Zaku iya kallon video anan domin kallonsa saiku click akan wannan

    

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Kannywood: Jarumi Ali Nuhu Ya Saki Zazzafan Fim Dinsa"

Post a Comment