Ana Kokarin Tsige Magu Daga Shugaban Hukumar EFCC (Karanta)

Mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa indai zai ci gaba da kasancewa a matsayin mukaddashin shugaban kasa, sannan shugaba Muhamadu Buhari a matsayin shugaban kasa, babu mai tsige Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa wato EFCC.

Ya kaddamar da hakan ne a Kaduna gurin kaddamar da ofishin hukumar EFCC na sashin.

A cewar Farfesa Yemi Osinbajo, “zai ci gaba da kasancewa shugaban hukumar EFCC idan har zan ci gaba da kasancewa mukaddashin shugaban kasa sannan shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasa.

Kukalli Wannan


SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ana Kokarin Tsige Magu Daga Shugaban Hukumar EFCC (Karanta)"

Post a Comment