Hadiza Gabon Tabawa Masu Yimata Tsegumin Tayi Aure Cikakkiyar Amsa

Fitacciyar jarumar Kannywood kuma kyakkyawa a fuska da jiki mai suna Hadiza Gabon ta yi karin haske game da masu yi mata nasiha da shagube akan wai taki tayi aure.

Jarumar bayan da maganganun suka je kunnen ta sai ta kada baki tace: “Shi aure lokaci ne kuma nufi ne na Allah, amma babu wata mace da zata yi fatan kaiwa kamar ni ba tare da tayi aure ba, kuma hankalin ta ya kwanta”

Amanagurus ta samu labarin cewa Hadiza Gabon din ta kuma ci gaba da cewa: “Saboda haka nima ina fata kuma ina adduar Allah ya kawo min miji nagari na samu nima in zama amarya.

Indai ba’a manta ba a kwanan baya ne tsohuwar fitacciyar jarumar ta Kannywood watau Safiya Musa ta fito tana mai bada shawarar cewa ya kamata yan matan fim din suyi aure.

Kukalli Wannan videon


SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Hadiza Gabon Tabawa Masu Yimata Tsegumin Tayi Aure Cikakkiyar Amsa"

Post a Comment