Adam Zango Yace An Taba Hana Shi Aure Saboda Ana Yimasa Zargin Yana Luwadi

A kasar Hausa dai, akwai wasu dabi’u da koda a wasu kasashen ba abun ki bane, suna iya jaza wa mutum jaa’i, cikin su kuwa harda zargin luwadi, neman maza dai a gwamnatance da shariar addini da ma al’ada, duk abun ki ne a fili.
A kimiyyance dai, masana sun ce auratayya ta jinsi bata da illa, ko ta madigo, ko ta luwadi, musamman zaman cewa a halittar wasu, akwai mata-maza, dama fahimtar menene sinadarin Oestrogen da Testosterone wanda ke cikin jini, wanda shi yake gaya wa kwakwalwa ita namiji ce ko mace, da ma cewa wa zata nema a matsayin abokin saduwa. Wannan, da ma masu halitta ta mace da namiji a jikinsu. Haka kuma a da ba’a tsangwamar ‘yan daudu, sai da aka fara shari’ar Islama a ‘yan shekarun nan.
A tsakanin al’umma ma dai, da anga wani ya faso gari, ko yayi kudi farat daya, sai a fara masa zargi ko na sata, ko tsafi, ko neman maza, ko ma hulda da wai aljannu. A haka sai a yi ta yi wa mutum sharri a kuma kyamace shi.
Hakan ta kai jarumi Adam Zango, da har sai da ya kai ga rantsuwa da Kur’ani, a lokuta da dama domin ya cire wa kansa wannan zargi, da jama’a ke yamadidi da shi, wanda a cewarsa, har aure aka taba hana shi bisa hakan.
‘Yan siyasa ma dai, da hamshakan malamai, ana musu irin wannan zargin, inda yakan zama kashin kaji da ake shafa musu don jama’a su kyamace su, wanda babu komai ciki sai bukulu da sharri.
Allah shi kyauta.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Adam Zango Yace An Taba Hana Shi Aure Saboda Ana Yimasa Zargin Yana Luwadi"

Post a Comment