Mazari Sarkin Rawa: Shin Zaku Yarda Ali Nuhu Zai Iya Daina Rawa Da Waƙa A Fim Kuwa?


Shahararren dan wasan Kwaikwayo na Kannywood Ali Nuhu wanda aka fi sani da Sarkin Kannywood ya bayyana ma BBC Hausa cewa ya kusa daina rawa da waka, amma fa sai idan lokaci yayi

Sarki Ali yace sau dayawa ya kan yi rawa da waka ne kadai idan hakan ya zama dole, musamman idan Fim din na bukatar ayi hakan.

Sarki Ali ya kara shaida ma majiyar Amanagurus cewar idan da za’a kwatan ta irin rawar da yake yi a baya, za’a gane cewa ya rage sosai.

Sai dai jarumin Fim din Hausan, wanda a yanzu shekarunsa 44 bai bayyana yaushe ne ranar da zai daina yin rawa ba. A wani hannun kuma a kwanan nan ne Ali Nuhu ya fitar da sabon Fim dinsa Mansoor, wanda masana suke ganin ya kawo sabon salo a Kannywood.

Kukalli Wannan videon


SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Mazari Sarkin Rawa: Shin Zaku Yarda Ali Nuhu Zai Iya Daina Rawa Da Waƙa A Fim Kuwa?"

Post a Comment