ABUBUWA GUDA GOMA WADANDA ZASU IYA JANYO MAKA CIWON QODA:

ABUBUWA GUDA GOMA WADANDA ZASU IYA JANYO MAKA CIWON QODA:

Matsayin Qoda ajikin 'Dan Adam,
kamar matsayin Carburetor ne ajikin Qarfe. Tana da muhimmiyar rawar da take takawa ajikin Dan Adam.

Mutane da yawa awannan zamanin suna fama da matsalar ciwonta. Don haka Zauren Fiqhu ya zakulo muku wasu abubuwa guda goma wadanda zamu kiyaye domin zama lafiya in shaAllah :

1. Rike fitsari na tsawon lokaci yana gajiyar da Qoda da sauran abubuwan dake aiki a mafitsarar Dan Adam.

2. Rashin shan ruwa akan lokaci shima matsala ce babba. Don haka duk lokacin da jikinka ya gaya maka yana bukatar ruwa, to ka bashi.

3. Yawan amfani da gishiri : Da yawa zaka ga mutane suna zamba'da gishiri acikin abinci, suna ganin kamar wata birgewa ce. To lallai sai akiyaye domin yin hakan zai iya janyo ma mutum matsala a Qodarsa.

4. Yawan cin abinci masu Qunshe da sinadarin Protein. Misali kamar Kifi, Nono, Qwai, Kitse, etc.

5. Rashin Magance matsalolin Infection akan lokaci (Wato irin chutukan da ake dauka ta hanyar Jima'i ko Qazantar bandaki, etc).

Shima infection idan ya dade sosai ba'a maganceshi ba, yana haurawa sama ya haifar da ciwon Qoda.

6. Yawan Kwankwadar giya (Barasa) da sauran Miyagun kwayoyi : Suna rikitar da ayyukan sinadaran jikin Dan Adam. Daga karshe kuma su haifar masa da ciwon Qoda.

7. Yawan amfani da abubuwan dake dauke da sinadarin caffeine (Kamar Goro, Coffee, Taba Weewi).

8. Yawan Amfani da magungunan kashe zafin ciwo wato Analgesics. Su ma saboda Qarfinsu suna iya haifar da ciwon Qoda.

9. Zukar taba Sigari shima yakan haifar da Sankarar Hunhu, sankarar zuciya, da kuma Qoda.

10. Rashin samun isashen barci shima yana iya haifar da matsalar Qoda. Domin zai zama tana aiki ne ba tare da hutawa ba. Daga karshe sai ta fara kumbura tana bada matsala.

Allah shi kiyayemu daga ciwon Qoda da sauran manyan chututtuka irinsa. Ameeen.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "ABUBUWA GUDA GOMA WADANDA ZASU IYA JANYO MAKA CIWON QODA:"

Post a Comment