Fina-finan Kannywood 12 da suka shahara a 2017

Duk da babban kalubalen matsalar satar fasaha da masana'antar finafinan Kannywood ke fuskanta, amma an fitar da fina-finai da dama a cikin shekarar 2017, da suka kunshi masu kayatarwa da marar kyau da matsakaita.Kuma kafin shekarar ta kawo karshe ana sa ran fitowar wasu sabbin fina-finai, kamar Juyin Sarauta, Sabon Dan Tijara, Dan Sarkin Agadaz, Mu Zuba Mu Gani, Dan Kukaa Birni da dai sauransu.Don haka daya ko biyu daga cikinsu na iya shiga sahun Fina-finan 2017.
1. There's a WayAna ganin wannan ne Fim na Inglishi na farko a masana'antar Kannywood,wanda furodusansa shi ne babban malamin Ingilishi Kabiru Jammaje, sannan Falalu Dorayi a matsayin darakta.Fim din ya bayar da labari ne akan gwagwarmaya tsakanin masu karamin karfi da attajirai.Fina-finan Kannywood 12 da suka shahara a 2017
An fito da halayyar wasu 'ya'yan attajirai a Jami'a da kuma rayuwar mata, wanda a haka aka tsara labarin.Soyayya ce tsakanin Isham (Nuhu Abdullahi) Dan talaka amma hazikin dalibi da kuma Fadila (Hajara Jalingo) 'yar wani babban hamshakin attajiri Alhaji Mahdi (SaniMu'azu) wanda ba ya kaunar hada zuri'a da talaka inda ya bi duk hanyoyin da zai bi domin ganin ya raba su.Ana sa ran This is the Way, zai fito kafin karshen shekara. Raunin Fim din shi ne karshensa da kuma amfanida salon harshe mai sarkakiya.Amma tsarin fim din baki dayansa yakayatar wanda hakan martani ne ga sukar da ake wa masu shirya finafinan Hausa cewa jahilai ne, da ba su iya da turanci ba.
2.Umar SandaKamal S. Alkali ne Daraktan Fim din, labarin ya mayar da hankali ne a kan mai ra'ayin rikau Umar Sanda (Ali Nuhu) da iyalinsa.Ko da yake ma'aikaci ne, kuma yana kokarin ganin iyalinsa na cikin wadata. Ana zaman lafiya har zuwa lokacin da 'yarsa ta hadu da wani abokin karatunta Dan shugaban 'Yansanda da aka shagwaba, wanda kuma ta kashe shi a kokarin kare kanta.
Umar Sanda ne ya binne gawar a yayin da 'yan sanda ke bincike mai tsauri.Duk da cewa an kwaikwayi fim din nedaga wani fim na Indiya, amma yadda aka tsara shi zai iya kasancewa daya daga cikin mafi shahara a bana. Ya nuna girman gaskiya da hadin kai da dabi'u masu kyau.
3.Ankon BikiAli Gumzak ne daraktan Fim din, kuma Ankon Biki ya mayar da hankali ne a kan muhimmin batu da ake fuskanta a yanzu.Mubarak (Adam Zango) da Fa'iza (Sadiya Bulala) suna shirin aure, sai Fa'iza ta kawo batun "Anko" da bukatar a hada wani babban bikin kasaita a wani wuri mai tsada.
Mubarak da abokansa sun yi iya kokarin ganin sun biya bukatar Amarya da kawayenta amma sun gagara, amma Amaryar ta dage a kan bukatar har ta bayar da kanta a madadin kudin kama wajen da za a yi bikin.
Ya fasa aurenta a ranar bikin bayan asirinta ya tonu, kuma a madadinta ya auri kawarta ta kud da kud. Fim din ya nuna girman nisan da wasu mata ke dauka don cimma bukatunsu.Duk da yake wasu wuraren a fitowar fim din na da tsayi amma an yi amfani da Hausa mai kyau da salon magana.Sauran taurarin fim din sun hada da Hafsar Idris da Umma Shehu da Al Amin Buhari da dai sauransu.
4.RariyaYaseen Auwal ne Daraktan Rariya, kuma fim na farko da Rahama Sadauta dauki nauyin fitowarsa, wato matsayin furodusa.Labarin Fim din ya danganta tasirin wayar salula ta zamani da ake kira"komi da ruwanka". Fim din ya shafi yadda wasu 'yan matan Jami'a ke amfani da wayar salula domin janyo hankalin maza.Yadda aka hada fim din ya kayatar. Babban muhimmin abu shi ne yadda daya daga cikin 'yan matan ta banbanta da saura inda har ta yi kokarin kammala karatunta.

Mutane da dama ba za su so haka ba, musamman iyaye da ke da'awar karatun 'ya'ya mata. Amma duk da haka linzamin labarin ya shafi abin da ke faruwa kuma ke shafar jama'a.Taurarin Fim din sun kunshi Ali Nuhuda Rabiu Rikadawa da Rahma Sadau da Fati Washa da Hafsar Idris da sauransu.
5.Mijin YarinyaAli Gumzak ne Darakta, kuma Mijin Yarinya ya shafi labarin wani Dattijo Attajiri Bashir Nayaya (Alhaji).Wata rana ya ji matansa guda biyu da Allah bai ba su haihuwa ba suna ma shi addu'ar mutuwa domin gadon dukiyarsa kuma don su aure yara samari, su yi sabuwar rayuwa.Saboda haka ne ya je ya auri budurwa Maryam Yahaya bayan ya saye imanin iyayenta da saurayinta da kudi.

Wannan ne ya fusata manyan 'ya'yansa Aminu Sharif da Sadiya Bulala, inda suka taya iyayensu matakishi.Bayan shafe lokaci ana makirci da takaddama, Alhaji ya yanke shawarar sakin dukkanin matansa, hadi da amaryarsa. Fim din na kunshe da darussa masu yawa a yadda aka tsara fim din.Sabuwar 'yar fim Maryam Yahya ta yikokari a fim din mai kunshe da gwanaye. Ba tare da zuzutawa ba fim din na cike da ban dariya da ilmantarwa.
6.Kalan DangiWannan ma wani fim ne na barkwanci da Ali Gumzak ya bada umurni wato a matsayin Darakta, Fim din ya nuna yadda talakawa ke neman arziki da kuma attajirai.Yayin da kuma masu arzikin ke kaskanta Talakawa. Ali Nuhu da Aminu Sharif da Sadiq Sani Sadiq da Jamila Nagudu da Fati Washa da Aisha Tsamiya na rayuwa ne ta nunaarziki da karya da makirci da nuna karfin iko. Idan kana neman nishadantarwa, to ka nemi Kalan Dangi.
Sai dai an raba fim din biyu, na daya da na biyu. Amma an takaita labarin da kuma karshensa, wanda ake sa ran fitarwa a shekara mai zuwa.Kamar taken fim din Karshen Kalan Dangi zai iya kawo karshen duk wanirikici.
7.Makaryaci Kamar sauran shahararrun fina-finanbarkwanci da aka fitar a 2017, Ali Gumzak ne daraktan Makaryaci.Sadiq Sani Sadiq ne da Allah ya ba basirar wasan kwaikwayo, ya daukaka fim din a matsayin daya daga cikin fitattu a bana. Labarin Fimdin ya shafi yadda kwadayinsa na dukiya ya kai shi ga samun kudi ba tare da ya sha wata wahala ba.Yakan je ya yi hayar tufafi ya harde cikin babbar motar mai gidan Rabiu Daushe ana tuka shi zuwa wurare har zuwa cikin Jami'a. Yakan yi wa dalibai karyar cewa shi dan gidan minista ne ko ambasada.

A hakan ne ya fara soyayya da daya daga cikin daliban Hafsat Idris. Ba tare da bin umurnin kakanninsa ba, ya je ya kadar da dabbobinsa na gado, domin ya kashe wa budurwarsa kudi wacce daga baya tagano asalinsa.Taurarin Fim din sun kunshi Sulaiman Bosho da Mama Tambaya da Mustapha Nabaruska da Musa Maisana'a da sauransu.
8.Husna ko HuznaHusna (Jamila Naguda da Abdul (Adam Zango) sun shirya yin aure, yayin da kuma Huzna (Fati Washa) tayi kokarin hana auren saboda matukar son da ta ke wa Abdul.A yayin da suke hamayya, wata rana Husna ta watsa wa Huzna guba a fuska, ba tare da sanin cewa ashe fatalwa ce. Washegari Huzna ta tafi gidansu ta mallaki Husna.Wannan ya bude wani sabon babin hamayya tsakaninsu inda Huzna ta shiga jikin Husna kuma ta ci gaba dazama a gidanta. Yadda aka tsara fim din ya ja hankali.

Amma duk da akwai matsaloli da akasamu, Fim din na iya zama daya daga cikin manyan fitattu finafinai a Kannywood.Fim din dai bai kasance wani abin muni ga mata ba, kamar yadda aka tsara labarin fim din irin na ban tsoro, a rikicin rayuwar aure tsakaninmata don mallakar namiji.Rawar da Washa ta taka ya kayatar. Falalu Dorayi ne Daraktan Fim din.
9.Burin FatimaWasu za su yi mamakin yadda wannan fim ya shigo sahunAmma duk da akwai matsaloli da akasamu, Fim din na iya zama daya daga cikin manyan fitattu finafinai a Kannywood.Fim din dai bai kasance wani abin muni ga mata ba, kamar yadda aka tsara labarin fim din irin na ban tsoro, a rikicin rayuwar aure tsakaninmata don mallakar namiji.Rawar da Washa ta taka ya kayatar. Falalu Dorayi ne Daraktan Fim din.9.Burin FatimaWasu za su yi mamakin yadda wannan fim ya shigo sahun fitattu. Ya cancanta. Labari ne akan wata matar aure da ta fada tarkon shawarar kawarta.Aisha Tsamiya tauraruwar fim din itace kuma ta dauki nauyin fitowarsa a matsayin furodusa.Fim din ya ba da labarin wata mata (Tsamiya) da mijinta, Adam Zango a yayin da ta ke makaranta, wata kawarta ta ba ta shawarar ta zubar da juna biyu da take dauke shi don tasamu sukunin karatu.. Ya cancanta. Labari ne akan wata matar aure da ta fada tarkon shawarar kawarta.Aisha Tsamiya tauraruwar fim din itace kuma ta dauki nauyin fitowarsa a matsayin furodusa.Fim din ya ba da labarin wata mata (Tsamiya) da mijinta, Adam Zango a yayin da ta ke makaranta, wata kawarta ta ba ta shawarar ta zubar da juna biyu da take dauke shi don tasamu sukunin karatu.
Ta karbi shawarar kuma ta yi wa mijinta karya cewa cikin ya bare, ba tare da sanin cewa ba ta kara haihuwa ba. Ta fuskanci kalubale daga sarakuwarta kan rashin haihuwa inda ta tursasawa Zango yakara aure.Ali Gumzak ne ya bayar umurni a fim din da ba a kashewa kudi ba. Sannanbai samu karbuwa ba.Amma ba don haka ba da zai kasance daya daga cikin finafinan dasuka samu karbuwa ga jama'a. Wannan dai ci gaba ne ga Tsamiya, kasancewar fim dinta na farko a matsayin furodusa.
10.MansoorFim din Mansoor na FKD yana cikin wadanda ake kururutawa a matsayin gwarzon shekara. Ali Nuhu ne Darakta.An fara fim din ne da soyayyar wasu matasa daliban makaranta, Maryam Yahaya da Umar M. Sharif.Amma mahaifin Sharif ne ya kawo karshen abotar, saboda yana zargin Sharif ba ya da uba, wanda wannan ya ba shi kwarin guiwar gudanar da bincike domin gano asalin mahaifinsa, ba tare da sanin cewa ashe gwamnan jiha ba ne mahaifinsa.
Labari ne ya mamaye fim din. Kuma ko shakka babu, fim din ya kasance kamar a zahiri. Baki dayan fim din ya shafi labarin matasan masoya tsakaninsu da iyayensu.An aiwatar da fim din da kyau. Taurarin fim din sun hada da Ali Nuhu da Abba El Mustapha da Baballe Hayatu da Teema Yola da daisauransu.
11.Dawo DawoFim din Kabuwagawa ne wanda Ali Gumzak ya bayar da umurni.Dawo-Dawo labari ne game da wasuda suka reni yaro (Adam Zango) tun kuriciya har girmansa inda suka kuma aurar ma shi da 'yarsu (Maryam Gidado).Amma daren farkon aurensu, amaryar ta yi karyar cewa tana da aljannu, ta tursasa ma shi ya sake ta.Nan take iyayen suka daura ma shi aure da kanwarta (Aisha Tsamiya).
Ita kuma (Gidado) ta koma ga tsohonsaurayinta (Zahraddeen Sani) wandasaboda shi ta kulla makircin. Daga baya ya yi watsi da ita, inda ta shiga wani hali ta koma kamar mahaukaciya lokacin da ta fahimci cewa ta dauke da cikin Zaharaddeen.Fim din na cike da makirci da rikici, kuma taurarin fim din Zango da Tsamiya da Gidado suna yi kokari sosai. Wannan ya sa fim din ya sha gaban takwarorinsa a bana.
12.Ta Faru ta KareAminu Saira ne daraktan Ta Faru ta Kare, labarin fim din ya shafi rayuwarHafsat Idris, gurguwa, makauniya amma 'yar attajiri, da kuma Aminu Sharif (Momo) wanda ya aure ta kuma yake cin amanarta yana kawo 'yan matansa a gidanta har zuwa lokacin da dubunsa ta cika.Inda Adam Zango, abokin wasanta wanda Momo ya yi wa kanwarsa ciki ya yake shi har ya fitar da shi daga gidan.

Fim din na tattare da nishadi. Hafsat Idris da ta fito mai nakasar jiki da kuma Momo sun yi kokari a rawar dasuka taka a fim din.Sauran taurarin fim din sun hada Hadiza Gabon da Hauwa Waraka da sauransu.




SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Fina-finan Kannywood 12 da suka shahara a 2017"

Post a Comment