ADAMU ZANGO YA KAFA TARIHI A KASAR KAMARU

Fitaccen Jarumin Finafinan HausaAdam A Zango ya zama dan wasa na farko da ya kafa tarihi a bangaren samun masoya a masana'antar shirya Finafinan Hausa ta Kannywood da ma Arewancin Nijeriya baki daya.
 Dan wasan wanda aka gayyata wasa a garin `Yaounde` na kasar Kamaru, a daren ranar asabar, 2 ga watan Disamba 2017 ya samu cincirodon masoya maza da mata da wadanda suka rika tururuwar zuwa gidan wasan domin yin tozali da gwanin na su, wanda dan wasan ya yi kiyasi da cewa akalla za su kai kimanin mutum dubu 10,000 wanda suka shiga gidan wasan. Wasu kuma cewa su ka yi mutanen da suka shiga gidan ba za su kirgu a saukake ba kawai dai jarumin ya kimanta ne. Wata majiya ta tabbatar mana da cewa sai da wurin wasan ya cika makil. Wanda hakan ya nuna cewa Adam A. Zango shi ne mutum na farko wanda ya taba tara dimbin mutanen da babu wanda ya taba tara su a tarihin masana'anatar fim ta kannywood

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "ADAMU ZANGO YA KAFA TARIHI A KASAR KAMARU"

Post a Comment