Mu ba mu yarda a dawo da Rahama Sadau ba – Kabiru Maikaba

Shugaban Hadaddiyar Kungiyar Masu Shirya Fina-Finan Hausa (MOPPAN), Alhaji Kabiru Mai Kaba ya ce ba su yarda da matakin gafartawa Rahama Sadau wanda hukumar tace fina-finan jihar Kano ta yi a makon jiya.
Mai Kaba ya mayar da martani ne ga shugaban hukumar tace fina-finai Isma’ila Na’abba Afakalla.
A ranar Talata ne Afakalla, ya shaida wa BBC cewa, a shirye suke su fara tace fina-finan da jarumar za ta rika fitowa a cikinsu da kuma wadanda take daukar nauyinsu.
A watan oktoban da ya gabata ne shahararriyar jarumar ta fito fili ta nemi gafarar duk wani mutum da bai ji dadi ba sakamakon fitowar da tayi a wani bidiyon waka tana ” Rungumar ” wani mawakin hausa Hip Hop wato ” Classiq “.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Mu ba mu yarda a dawo da Rahama Sadau ba – Kabiru Maikaba"

Post a Comment