Shugaban hukumar FBI ne ya yi min kafar ungulu-Clinton

Hillary Clinton ta zargi shugaban hukumar FBI
James Comey, da taka muhimmiyar rawa a shan
kayen da ta yi a zaben shugaban kasa da aka
kammala a makon da ya wuce.
Misis Clinton dai ta shaidawa jiga-jigan jam'iyyar
ta cewa sanarwar da Mista Comey ya yi na bata
da laifi kan batun amfani da Email din ta a
lokacin da ta ke Sakatariyar harkokin wajen
Amurka, kuma a kurarren lokaci shi ya yi wa
nasarar ta kafar ungulu ta fuskar rage magoya
bayan ta.
A bangare guda kuma dubban Amurkawa a sassa
daban daban ne ke ci gaba da boren kin
amincewa da Mista Trump a matsayin shugaban
kasa.
A birnin New York 'yan sanda sun yi kokari hana
masu zanga-zangar isa dandalin Union, da wasu
kuma na daban da suka tunkari gidan Mista
Trump da kuma dogon ginin Trump Towers da
hedikwatar kasuwanci da ke birnin.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Shugaban hukumar FBI ne ya yi min kafar ungulu-Clinton"

Post a Comment