Inter Milan ta kori kociyanta de Boer

Inter Milan ta sallami kociyanta Frank de Boer,
bayan da ya jagoranci kungiyar kwanaki 85.
De Boer ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara
uku a Inter a watan Agusta, bayan da ya maye
gurbin tsohon kociyan Manchester City, Roberto
Mancini.
Inter tana mataki na 12 a kan teburin gasar Seria
A ta Italiya, inda ta yi rashin nasara a hannun
Sampdoria da ci 1-0 a ranar Lahadi, kuma wasa
na hudu da aka doke ta daga guda biyar da ta yi.
Kungiyar ta nada mai horar da matasan 'yan
kwallonta, Stefano Vecchi a matsayin kociyan
rikon kwarya.
Kungiyar mai buga gasar Italiya na neman mai
horar da 'yan wasa karo na tara tun bayan da
Mourinho ya bar Inter a shekarar 2010.
Wadan da suka horar da Inter a cikin shekara
shida sun hada da kociyan Newcastle United,
Rafael Benitez da Claudio Ranieri na Leicester
City da kuma mai jan ragamar Watford Walter
Mazzarri.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Inter Milan ta kori kociyanta de Boer"

Post a Comment