'Yan Niger Delta sun mika bukatunsu ga gwamnati

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana
da shugabannin yankin Niger Delta, da nufin
kawo karshen hare-haren masu tada kayar baya
kan bututan mai a yankin.
Shugaba Muhammadu Buhari ya shaida wa
tawagar shugabannin yankin Neja - Delta, cewa
matsalar da gwamnatin sa ta tarar a lokacin da
ta karbi mulki suna da yawan gaske, wadanda
suka hada da faduwar farashin man, da rashin
iya biyan albashi da wasu jihohi 27 daga cikin
jihohi 36 na kasar.
Sauran Matsalolin a cewar shugaban Najeriyar
sun hada da rashin tattalin dan abun da kasar ke
samu, lamarin da ya ce ba bu yadda za'a yi a ci
gaba da tafiya a haka.
Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya karbi
wasu jerin bukatu 16 da tawagar ta gabatar
masa, ya ce ya na jiran rahoton wani kwamitin
da ya dorawa alhaki sake nazari akan shirin yi
afuwa ga tsegurun yankin Neja Delta, inda daga
nan ne gwamnatin sa zata ga bangaren da ta
gaza domin yin gyara.
Jerin bukatun da tagawar ta gabatar sun hada da
gaggauta kammala manyan hanyoyin da aka fara
a yankin da kuma maida hedkwatar manyan
kamfanonin mai a Nigeriar zuwa yankin Niger
Delta, matakin da a cewar su zai taimaka wajen
kara samar da ci gaba a yankin.
Shugabannin yankin Niger Deltan karkashin
jagorancin Chief Edwin Clerk sun kuma bukaci
gwamnatin tarayya data gaggawa share
dagwalon mai daya mamaye wasu garuruwa a
yankin baya ga yankin Ogoni.
Haka kuma Shugabannin sun nemi gwamnati da
ta sake duba shirin afuwa ga tsagerun yankin
tare da tabbatar da cewa an samar da ayyukan
yi ga wadanda aka horas da su karkashin shirin
yin afuwa ko kuma a rika basu dan abun hasafi.
Sun kuma dau alwashin ci gaba da tattauna wa
akai-akai a jihohi daban-daban na yankin a wani
mataki da ganin an samu dorewar zaman lafiya.
Sannan suka ce tuni aka fara ganin tasirin
tattaunawar da suke yi tsakanin su wanda hakan
ya kai ga yanzu aka samu karuwar danyen mai
da ake hakowa zuwa ganga miliyan 2 da dubu
100.
Tawagar karkashin kungiyar Pan Niger Delta
Forum sun kuma jaddada goyon bayan su ga
Shugaba Buhari bisa abin da suka ce kokarin
gwamnatin sa wajen tabbatar da hadin kan
al'ummar Nigeria a matsayin kasa daya.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "'Yan Niger Delta sun mika bukatunsu ga gwamnati"

Post a Comment