Dakarun Iraqi na luguden wuta a cikin birnin Mosul

Dakarun gwamnatin Iraqi da suka kutsa cikin
birnin Mosul, da a karon farko tun bayan
kungiyar masu ikirarin jihadi ta IS sun karbe shi
shekaru biyu da suka gabata, sun ce za su ci
gaba da dannawa cikin birnin har sai baki
dayansa ya dawo karkashin ikon gwamnati.
Mai magana da yawun sojojin Iaraqin Sabah al-
Numan, ya shaidawa BBC cewa a yanzu dakarun
su a shirye suke tsaf dan fara yaakin ta hanyar
binciken kowannen gida.
Al-Numan ya kara da cewa duk da bata kashin
da aka yi a jiya talata, wanda har aka yi nasarar
kwato gidan talabijin da ke yammacin birnin
Mosul da 'yan IS suka karbe iko da shi, dakarun
su kalau suke ba tare da jin ko rauni ba.
Wakilin BBC da ke cikin tawagar su ya ce babu
alamar sassauta ruwan bama-baman da sojiji ke
yi, a daidai lokacin da suke kara dannawa dan
fatattakar 'yan tawaye daga cikinsa.
Sai dai a nata bangaren MDD ta nuna damuwa
kan makomar sama da fararen hula miliyan daya
da ke suka makale a cikin birnin.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Dakarun Iraqi na luguden wuta a cikin birnin Mosul"

Post a Comment