
Shahararren jarumin nan kuma furodusa Zaharadeen Sani ya ce ya samu amincewar hukumar ‘yan sandan farin kaya DSS tare da hukumar tantance fina finai ta kasa domin ya shirya fim da ke nuna rikicin Boko Haram.
A wata hira da yayi da jaridar Premium Times, Zaharadeen ya ce ya fuskanci kalubale da farko domin hukumar tantance fina finai ba ta amince da fim din ba saboda irin tufafin ‘yan ta’addan da aka yi amfani da su da kuma bindigogi da khakin sojoji.
Ya ce haka kuma ya samu gayyata daga DSS domjn ya zo ya kare dalilansa na shirya fim din.
Zaharadeen ya ce ya shirya fim din ne saboda ya nunawa mutane illar da rikicin Boko Haram ya haifar a kasar nan, wanda da shi ne yake kwana da shi yake tashi.
Fim din mai suna ABU HASSAN dai ana hasashen cewa ba a taba yin irin sa ba a Kannywood.
Labarin ya nuna wata kungiyar ta’addanci da ta addabi mutane wacce sojoji suka ci lagwanta daga karshe.
Related Posts :
'Rahama Sadau ki tuba: Har yanzu baki makara ba'>>Bello Muhammad Bello
Bayan taya Rahama Sadau murnar samun kyautar da aka bata a kasar Amurka, Bello Muhammad Bello, General BMB yayi kira ga Rahamar da tayi a… ...
Karanta amsar da Rahama Sadau ta baiwa wani da yace mata ya kamata tayi aure
Wani bawan Allah ya shawarci tauraruwar fina-finan Hausa da turanci Rahama Sadau da cewa ya kamata tayi aure, Rahamar ta bashi amsa da ce… ...
Kukaranta kuji; shahararren mawakin hausa wato nura m inuwa yaje aiki umrah
Tauraron mawakin Hausa, Nura M. Inuwa yaje aikin Umrah, muna mishi fatan Allah ya amsa Ibada ya kuma dawo dashi gida lafiya.
… ...
Rahama Sadau Yar Kwalisa
Tauraruwar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau kenan a wannan hoton nata da tayi shigar gayu, tasha kyau, Muna mata fatan Alheri.
… ...
Rahama Sadau ta zargi jakadan Najeriya a kasar Turkiyya da hana sarkin Kano kaiwa dalibai ziyara a kasar Cyprus
Tauraruwar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau karkashin daliban dake karatu a jami'ar Eastern mediterranean ta kasar Cyprus, ta za… ...
0 Response to "KANNYWOOD: JARUMI ZAHARADDEEN SANI YA SHIRYA WANI SABON FIM MAI NUNA RIKICIN BOKO HARAM"
Post a Comment