
Hadiza Gabon ta aike sakon ne ta shafinta na Instagram
Fitacciyar 'yar wasar Hausan nan Hadiza Gabon, ta yi gargadi ga magulmata masu yawan magana a kan 'yan wasan Hausa a shafukan sada zumunta.I'll
Hadiza ta aike da sakon ne ta shafinta na instagram inda ta ce, "Ina mamakin yadda mutane suke shiga abin da babu ruwansu."
Ta kara da cewa, "Masoyinka ba zai zage ka ba, sai dai ya baka shawara, kuma mu 'yan wasan Hausa muna maraba da shawarwari daga wajen masoya amma bai kamata mutane su dinga gulmace-gulmace da fadin abubuwan da bai shafe su ba.
Gabon ta ce ya kamata mutane su bi koyarwar addinin Musulunci su daina gulma da bin diddigin da ba huruminsu ba da kuma shiga sharo ba shanu.
Ta dai yi wannan magana ne sakamakon yadda wasu mutane ke aikewa da sakon zagi da cin zarafi a duk lokacin da 'yan wasan suka sanya wani abu da ya shafe su a shafukan sada zumunta.
Hadiza ta ce, idan ma gyara ake so a yi musu to ya kamata a yi cikin girmama juna da fahimta.
Related Posts :
Ina Sa Ran Dawowa Harkar Fim Gadan-gadan – Inji Zainab Indomie
Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana’antar Kannywood wadda aka fi sani da Zainab Indomie ta bayyana cewa tana sa ran zata … ...
Fulani Siddika Sanusi na murnar zagayowar ranar haihuwarta
Diyar Sarkin Kano, Fulani Siddika Sanusi na murnar zagayowar ranar haihuwarta a yau, muna tayata murna da fatan Allah ya karo shekaru mas… ...
Yakubu Muhammad Rahama Sadau da Amal Umar a Legas
Jaruman fim din Hausa da kuma suke taka rawar gani a finfinan yankin kudu, Yakubu Muhammad da Rahama Sadau, kai ba dankwali, da Amal Umar… ...
Fatima Sulaiman na murnar zagayowar ranar haihuwarta
Jarumar fim din Hausa, Fatima Sulaiman na murnar zagayowar ranar haihuwarta, Muna tayata murna da fatan Allah ya karo shekaru masu albark… ...
>Ummi Zeezee" href="https://amanagurus.blogspot.com/2017/09/idan-budurwarka-ba-kanuri-bace-to-baka.html">"Idan budurwarka ba Kanuri bace to baka da budurwa" >>Ummi Zeezee
Jarumar fim din Hausa, Ummi Zeezee kenan a wannan hoton nata da yayi kyau, saidai kai ba dankwali, Ummi ta saka wannan hoton nata a danda… ...
0 Response to "KANNYWOOD: MAGULMATA SUN FUSATA JARUMA HADIZA GABON"
Post a Comment