Shin Ko Dan Zina Yanada Gadon Mahaifiyar Sa ? Sheikh Jamilu Yusuf Zarewa.

 sheikh Jamilu Yusuf Zarewa

Shin Ko Dan Zina Yanada Gadon Mahaifiyar Sa Sheik Jamilu Yusuf Zarewa - Fatwah

Tambaya ?

Assalamu alaykum. Malam don Allah Malam innada tanbaya, Malam mace ce tayi cikin batare da aure ba, ta haihu kuma tana da kudi sai Allah yamata rasuwa toh malam yaron zaici gadonta. 

Amsa: 

Wa alaikum assalam, idan mace ta yi cikin shege kuma ta haifi Da, daga baya ta mutu Dan zinar da ta haifa zai gaje ta, saboda Allah madaukakin sarki a cikin suratun Nisa'i aya ta : 10 ya yi wasiyya a bawa 'ya'yaye gado, Dan zina kuma yana cikin jerin 'ya'yayen mahaifiyarsa, wannan yasa zai gaje ta.

Dan zina ba ya gadon mahaifinsa a wajan mafi yawancin malamai, ko da kuwa ya yarda dansa ne. 

Allah ne mafi sani.Dr Jamilu Zarewa.

® Sheikh DR.Jamilu Yusuf Zarewa

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Shin Ko Dan Zina Yanada Gadon Mahaifiyar Sa ? Sheikh Jamilu Yusuf Zarewa."

Post a Comment