Takai Taccen Tarihin Mawaki Umar M Shareef





Tarihina a takaice

Assalamu alaikum, sunana Umar Muhammad Sharif, an haife ni a Rigasa da ke Jihar Kaduna a shekarar 1987. Na yi makarantar firamare da sakandare duk a Rigasa. 

Dalilin da ya sa na zabi sana’ar waka

Waka ta fado mini kwatsam da rana tsaka ne, amma a gaskiya ban taba tunanin zan yi sana’ar waka ba, saboda tun tasowata ni dalibi ne, ina karatun boko da na addini, na ma fi ba da karfi a bangaren addini. Silar fara waka kuwa ita ce akwai wata budurwa da nake matukar so da kauna, amma na kasa sanar da ita abin da ke zuciyata.

A gaskiya jin nauyin abin shi ne ya hana ni sanar da ita. Nakan je har kofar gidansu, na aika a yi mini sallama da ita, amma inda gizo ke sakar shi ne da zarar ta fito don ganin wanda ke neman ta, sai na buya, ta gama dube-dubenta daga nan idan ba ta ga kowa ba sai ta koma gida.

To na yi hakan kusan har sau uku ba tare da samun damar tsayawa da ita ba. Daga nan wata rana sai na yi ta maza na ce zan ga abin da zai ture wa buzu nadi. 

Da na je sai na aika kamar yadda na saba amma sai a wannan karon ba ta fito ba. Na yi ta jira amma shiru kake ji.

To daga nan ne fa kamar wasa sai na fara yin waka a kan halin da na samu kaina ciki. Daga kofar gidansu na fara waka har na isa gida ban daina ba. Haka na yi tayi duk lokacin na tuna da wannan baiwar Allah.

A cikin wannan halin ne sai na samu biro da takarda na rubuta wakar. Akwai wani mawaki Ibrahim Suleiman (Zaki) wanda ya kasance abokin yayana ne. Kamar wasa da ya ga wakar kuma ya umarce na rera ta. Bayan ya saurari wakar sai ya yaba kuma ya yi min wasu gyararraki, kana ya karantar da ni kabli da ba’adin waka. Daga nan ne fa na fara waka gadan-gadan.

Kalubale

Da farko na fuskanci kalubale daga gida, daga bisani muka fahimtar da iyayenmu. Bayan ba su ga canji daga irin tarbiyyar da suka yi mana ba, sai suka fara sa mana albarka da fatan alheri. Shakka babu addu’o’insu na tasirin sosai a kan nasarorin da muke ci gaba da samu.

Wakokin da na yi

A kalla wakokina za su kai 700

Kundin waka

Akwai su kamar haka: ‘Duniya Ce’ da ‘Nadiya’ da ‘Shahuda’ da ‘Madubi’ ‘Mai Atamfa’ ‘Babbar Yarinya’ ‘Wacece’ ‘Kalaman Bakina’ ‘Bako’ Da dai sauran su...

Bakandamiyata
Duka wakokina.

Fitowa a fim

Ina fitowa a fim, sannan nakan shirya nawa. Fina-finan da na fito sun hada da: ‘Mahaifiyata’ da ‘Nas’. Fina-finan da na shirya sun hada da: ‘Ba Zan Barki Ba’ ’Ka So A So ka’ da ’Jinin Jikina ’ Sannan Akwai Wani Film Dana Fito A Cikin sa a wannan shekarar Mai suna Mansoor.

Burina

Ba ni da wani burina saboda ko yanzu kasuwa ta watse dan koli ya ci riba. Sunana ya kai duk inda ba ka zato, saboda na sha samun kira ta waya daga Amurka da sauran kasashen duniya, wanda jama’a ne masu sauraren wakokinmu ke yaba mana.

Iyali

Ina da mata daya Maryam da da daya ana kiransa Aliyu.

Source : www.HausaMedia.Com

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Takai Taccen Tarihin Mawaki Umar M Shareef"

Post a Comment