Ana zargin Sanchez da kin biyan haraji

Masu shigar da kara a Spaniya na zargin Alexis
Sanchez da kin biyan haraji a lokacin da yake
kungiyar kwallon kafa ta Barcelona.
Masu shigar da karar sun ce Sanchez mai
shekara 27, bai biya harajin kudin da ya kai fam
£888,246 daga tsakanin shekarar 2012 da 2013.
Sun kuma ce dan kwallon ya yi amfani ne da
wani kamfani a Malta domin yin rufa-rufar harajin
da za a caje shi kan kudaden talla da yake samu
a fagen tamaula.
Sanchez ya koma Arsenal da Murza-leda daga
Barcelona kan kudi fam miliyan 35 a shekarar
2014.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ana zargin Sanchez da kin biyan haraji"

Post a Comment