"Ba maza bane kawai basa iya rike sha'awarsuba:Mata ma na bukatar maza Hudu"

A jiyane labarin wata baiwar Allah data kashe mijinta saboda tsabar kishi ya watsu a kafafen labarai, musamman ganin cewa duka matar ta mijin sun fito daga manyan gidaje a kasarnan, hakan ya kara sa labarin ya dauki hankulan mutane sosai, tun bayan aukuwar lamarinne sai jama'a akaita kara jawo hankulan, musamman mata da su tuna cewa addinin musulunci ya baiwa namiji damar yin mata hudu saboda haka su daina zafin kishin da zai kaisu ya baro.
Wannan baiwar Allah da hotonta ke sama taci karo da irin wannan fadakarwar dake jawo hankalin mata akan cewa auren mace daya mutum yace bazai karaba/ watau bawai dan baya ra'ayiba kawai ya takura kanshi kuma alhalin yana da halin, al'adar turawan jammace.
Kada bakin da zatayi sai tace ai Allahma be halittawa Annabi Adamu Hauwa fiye da daya ba, saboda haka mata su daina tunanin cewa suma ba zasu iya jin dadin rayuwa ba(ko me take nufi da hakan?) Su rike baiwa maza damar yin abinda suka ga dama ba(kara aure, yin budurwa). Taci gaba da cewa bafa mazane kawai basa iya rike sha'awarsu ba, mata ma suna bukatar maza hudu. Duk da yake cewa hakan ba abu bane me yiyuwa ba.
Bayan da wannan baiwar Allah tayi wannan rubutune sai hankulan mutane ya koma kanta.
Aka rika tambayarta wane irin addinin musulunci take yi? Wasu kuma suka rika gayamata ya kamata ta koma makarantar isilamiya, wani kuwa cewa yayi ai beyi mamakin jin wannan kalamai daga bakin wannan baiwar Allahn ba duba da irin yanayin yanda ta saka hoto a Duniya kowa na kallonta kai ba dan kwali.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to ""Ba maza bane kawai basa iya rike sha'awarsuba:Mata ma na bukatar maza Hudu""

Post a Comment