Jaruman Kannywood 5 dake da mukamin sarauta a masarauta daban daban

Jaruman Kannywood 5 dake da mukamin sarauta a masarauta daban daban

Kamar yadda kuka sani ba’a bar dandalin kannywood a baya ba ta fannin sarautar gargajiya wanda ke daraja martabar yankin arewacin kasar.

Munyi amfani da wannan damar wajen kawo maku wasu daga cikin jarumai biyar da suka samu sarauta a baya-baya nan
Ga jerin jaruman da mukaman sarautarsu a kasa:
1. Muhammad Ibrahim Mandawari
Wannan shahararren tsohon jarumi da yayi fice a dandalin Kannywood ya gaji mahaifin sa inda Sarkin Kano Mai Martaba Muhammad Sanusi na II ya nada shi a matsayin “Mai unguwar yankin Mandawari dake garin kano.
2. Sani Musa Danja
Dan zaki kamar yadda aka fi sanin jarumin da shi yayi bikin nadin sarautar “Zakin yan wasan Arewa” wanda sarkin Nupawa ya nada masa a jihar Niger.
Etsu Nupe ya nada masa wannan sarautar a ranar 25 ga watan Agusta a nan garin Bida.
3. Maryam Gidado
Kungiyar masu shirya fina-finai ta arewa na Arewa ta nada ta a matsayin “Innawuron Zamfara” ranar 4 ga watan Nuwamba a Gusau babban birnin jihar Zamfara.
4. Rasheeda Abdullahi Mai sa’a
A nata bangaren Jaruma Rasheeda mai sa’a ta samu sarautar “Wakiliyar arewa” daga kungiyar AFMAN a garin Minna babban birnin jihar Niger cikin watan Octoba na bana.
5. Fati Nijar
Daga karshe an ba mawakiya Binta Labaran wacce aka fi sani da fati Nijar sarautar “Gimbiyar arewa” a garin Minna, jihar Niger.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Jaruman Kannywood 5 dake da mukamin sarauta a masarauta daban daban"

Post a Comment