Jami'an hukumar EFCC da yan sanda sun gwabza da jami'an DSS da na NIA

Yayin da jami'an suka isa titin Nasir dake nan Asokoro domin gabatar da abun da ya kawo su, jami'an dake tsaron gidajen Oke da Ekpeyong sun ana su shigowa gidan ganin haka rikici ya barke tsakanin su.
Tawagar jami'an hukumar hana cin hanci da rashawa ta EFCC da jami'an yan sanda sun gwabza da jami'an hukumar DSS da na hukumar adana bayanai na sirri ta NIA ranar yau talata 21 ga watan nuwamba a garin Abuja.
A bisa labarin da jaridar premium times ta fitar, lamarin ya faru ne yayin da jami'an hukumar EFCC tare da taimakon wasu yan sanda suka nemi su kama tsohon shugaban hukumar NIA Ayodele Oke da tsohon shugaban hukumar DSS
Ita Ekpeyong a gidajen su dake nan birnin tarayya.
Yayin da jami'an suka isa titin Nasir dake nan Asokoro domin gabatar da abun da ya kawo su, jami'an dake tsaron gidajen Oke da Ekpeyong sun ana su shigowa gidan ganin haka rikici ya barke tsakanin su.
Rigimar dai ya haifar da ture-turen wucewar motoci a yankin.
An sallame Oke daga aiki ranar 30 ga watan octoba dangane da sa hannun sa ga kudin da barayin gwamanati suka wawushe wanda aka gano a wani gida dake nan garin Ikoyi na jihar Legas wanda hukumar EFCC ta gano.
Ana neman Oke tare da matar sa Folasade ofishin hukumar domin bada amsar tambayoyi daya danganci kudin da aka gano a jihar Legas.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Jami'an hukumar EFCC da yan sanda sun gwabza da jami'an DSS da na NIA"

Post a Comment