Matata ce amma a cikin shirin fim

A cikin wani sabon shirin fim jaruma Gabon ta fito a matsayin matar shi.
Fitaccen jarumi kuma babban direkta fina-finan hausa na masana'antar Kannywood Ali Nuhu ya musanta jita-jita dake yaduwa na cewa ya auri jaruma Hadiza Gabon a asirce bisa ga hoton su dake yawo a kafafen sada zumunta.
Hoton wanda jama'a ke tsegumi akan shi an dauke shine yayin da suke shirya wani sabon fim mai suna "Akushi".
A cikin shirin jaruma Gabon ta fito ne a matsayin matar shi.
"Sarkin kannywood" kamar yanda aka yi mai lakabi yayi kira ga jama'a da su daina yada jita-jita wanda bai da asali.
A matsayin su na yan fim ire-ire hotunan da suka dauka zai cigaba da fitowa don inganta shirirn fim da suke neman fitar domin nishadantar da masu bibiyan fina-finan kannywood.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Matata ce amma a cikin shirin fim"

Post a Comment