Dalilan Da Yasa Ali Nuhu Ya Karfafawa Rahama Sadau Wajan Bada Hakuri

Fitaccen jarumin Kannywood, Ali Nuhu ya kasance mutumin da ya karfafa wa korarriyar jaruma Rahama Sadau gwiwar ba gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi II hakuri kan al’amarin da ya kai ga dakatar da ita daga masana’antar shirya fina-finan Hausa a shekarar bara.
Ku tuna cewa kungiyar kula da ladabtar da masu shirya fina-finai wato MOPPAN ta yanke hukuncin korar jarumar bayan ta bayyana a wani kasetin waka wanda bai dace ba tare da mawakin Jos ClassiQ.
Ali Nuhu wanda yayi magana da jaridar Daily Trust akan wayan tarho yayinda yake shirin barin kasar ya bayyana cewa jarumar ta yanke shawarar bayar da hakuri ne bayan ta gane kuskurenta ya kara da cewa dan Adam ajizi ne.
“A matsayinmu na manya a masana’antar shirya fina-finai, hakki ne da ya rataya a wuyanmu domin kula da na kasa damu wannan ne dalilin da yasa na jajirce wajen bada hakurin ta.
“A rayuwa yana da kyau mutun ya gyara sannan ya bada hakuri a duk lokacin da ya saba. Rahama ta yi jarumta wajen bayar da hakurinta sannan kuma tayi alkawari bazata sake aikata wannan laifi ba kuma. Ta rubuta wasikar ban hakuri zuwa ga kungiyar MOPPAN wanda na tabbata a yanzu haka jami’an kungiyar na tattaunawa aka” cewar Ali Nuhu.
A daren ranar Talata, 24 ga watan Oktoba, da take magana a wani shirin gidan radiyo mai taken “Ku Karkade Kunnuwan Ku” wanda ake gabatarwa a shahararren gidan radiyo a garin Kano, Radio Rahama, jarumar ta sha alwashin cewa irin haka ba zai sake faruwa ba.

©arewablog.com

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Dalilan Da Yasa Ali Nuhu Ya Karfafawa Rahama Sadau Wajan Bada Hakuri"

Post a Comment