Babbar Matsalar Matan Film Bakin Ciki Da Kishi - In Ji Rahama Sadau

Babbar Matsalar Matan Film Bakin Ciki Da Kishi - In Ji Rahama Sadau
Daga Auwal M. Kura
Korarriyar 'yar wasan shirya finafinan Hausar nan kuma haifaffiyar garin Kaduna wato Rahama Ibrahim Sadau ta bayyana bakin ciki da kuma hasada a matsayin babbar matsalar da ta da baibaiye matan dake cikin masana'antar fim ta Kannywood.
Ta kuma yi zargin cewa da yawa daga cikin matan suna da girman kai, sannan suna amfani da sana'ar wajen biya wa kansu bukatun su kuma hakan ba karamin zubar wa da 'yan fim da daraja yake yi ba -in ji Rahama Sadau.
Babu shakka wannan babban kalubale ne dake bukatar sabbin shugabannin kungiyar masu shirya finafinai ta MOPPAN da aka zaba a karshen makon da ya gabata, su fara karyawa da shi, domin kara inganta darajar harkar fim din Hausa

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Babbar Matsalar Matan Film Bakin Ciki Da Kishi - In Ji Rahama Sadau"

Post a Comment