"Ina takaicin yanda wasu suka zama mabarata a shafukan sada zumunta na fitattun mutane">>Hadiza Gabon

Fitacciyar jarumar finafinan Hausa Hadiza Gabon ta bayyana rashin jindadinta akan irin yanda wasu suka mayar da shafukan sada zumunta na fitattun mutane irinta gurin bara da deman taimako, Hadiza tace bawai tana magana akan nemawa marasa galihu taimako da wasu masu kyakkyawar niyya keyi ba, tace tana magana akan masu kutsawa shafukansu suna aika musu da sakonnin neman taimkon kudi dan yin gyaran waya da wasu abubuwa dai da bana doleba.
Hadizar tace wasu suna ganin cewa fitattun mutane irinta suna da wani rumbum kudine wanda saidai kawai suyita daukowa suna baiwa mutane ba tare da matsalaba. Hadiza tace irin mutanennan ko kunya basa ji? Su rika tambayar mutumin da basu sanshiba kudi kuma bawai basu da lafiya bane ko kuma suna jin yunwaba.
Allah yasa irin masu irin Wannan halin sudena
Ameen

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to ""Ina takaicin yanda wasu suka zama mabarata a shafukan sada zumunta na fitattun mutane">>Hadiza Gabon"

Post a Comment