2016 za ta kasance mafi zafi a tarihi

Shekara ta 2016 za ta kasance shekara mafi
zafi a duniya tun lokacin da aka fara adana
bayanai kan yanayi, kamar yadda hukumar kula
da yanayi ta duniya ta sanar.
Hukumar kula da yanayi ta duniya ce ta ba da
sanarwar a wajen wani taron duniya kan yanayi
da ake yi a Morocco.
Wakilai a wajen taron na duba yadda zaben
Donald Trump a matsayin shugaban Amurka zai
shafi yarjejeniya kan dumamar yanayin duniya da
aka cimma a Paris a bara.
Sai dai kuma wakilin Amurka na musamman a
wajen taron, Jonathan Pershing, ya ce Amurka
za ta ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar Paris din,
duk da sauyin gwamnatin da aka samu.
Mr Trump ya taba bayyana sauyin yanayi a
matsayin wani abu da babu gaskiya a cikinsa,
wanda China ta kirkira domin lalata
masana'antun Amurka.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "2016 za ta kasance mafi zafi a tarihi"

Post a Comment