‘Nayi lalata da diyata domin in samu kudi’ - inji uba

wani magidanci ya shiga hannun hukuma bayan yayi lalata da diyar sa bisa ga umarnin bokaye
An gurfanar da wani magidanci Bashiru Adeyanju a gaban kotun majistere dake Ado-ekiti a jihar Ekiti bayan ya amince cewa yayi lalata da diyar shi mai shekaru 17 bisa ga umarnin bokaye domin ya samu arziki.
Bisa ga rahoton Tribune , Adeyanju ya amsa laifi cewa yayi lalata da diyar kusan so 9 kana bokayen suma sunyi farna da ita duk cikin tsarin neman kudi ta hanyar tsubbu.
Adeyanju wanda yace neman arziki yasa yayi lalata da diyar sa kuma bai ji dadi ba ganin cewa shi kadai aka gurfanar gaban ko yayin da bokayen suka tsere.
“Mu uku muka aikata laifi, amma nayi mamaki da na gana ni kadai yan sanda suka gurfanar a gaban kotu” inji adeyanju.
Shugaban kotun Mrs Dolapo Akosile ta tabbatyar mai cewa za’a gabatar da saura abokan aikin shi.
“Kada ka damu, za’a kawo saura gaban kotu”.
A bisa ga labarin Adeyanju, akwai wata farar kyallen hankicif da yake shafar farjin diyar duk lokacin da ya sadu da ita kamar yanda bokayen suka umarce shi, duk da cewa ya aikata haka lokaci da dama shidai wannan magidancin bai cinma burinsa na samun arziki.
Jami’in dan sanda da ta gurfanar da shi
Sergeant Monica Ikebuilo tace wanda ake tuhuma ya aikata laifi da ya sabawa kundin tsarin mulkin jihar kuma ta roki kotu da a daga karar har zuwa lokacin da hukumar dake yanke hukunci ta bada shawara akan laifin.
Shugaban kotu ya bada umarni na a cigaba da rikon mai laifin a gidan yari har zuwa ranar 12 ga watan Octoba bayan anji shawarar hukumar zata bada.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "‘Nayi lalata da diyata domin in samu kudi’ - inji uba"

Post a Comment