Rahma Sadau na dab da shiga sahun Jaruman da suka fi shahara a finafinan Kudu

Korarriyar jarumar finafinan Hausa da aka kora ta koma yin finafinan Turanci na kudancin kasar nan, Rahama Sadau ta kara samun wata gagarumar cigaba a harkar shirin fim din kudu da take yi.
Rahama Sadau dai ta shiga cikin wadanda za su lashe gasar fitattun jaruman finafinan Turanci na Kudu wanda ake kira da BON a takaice.
Tun dai bayan korarta da aka yi daga finafinan Hausa likafarta take ta ci gaba take kuma kara samun hawa matsayi kala-kala a harkar finafinai.
A cikin wata hira da Rahama ta yi kwanaki da jaridar ThisdayStyle ta ce duk abinda za ta yi ta kan yi kokari ta kare mutuncin addininta da kuma yankin da ta fito.
Daga shafin: Rariya

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Rahma Sadau na dab da shiga sahun Jaruman da suka fi shahara a finafinan Kudu"

Post a Comment