Sojoji sun kashe wani dan fashi, an gano bidigar AK 47 guda 2

Rundunar sojoji na 1 Division sun kashe wani daga cikin yan fashi da makami a karamar hukumar Tsafe na jihar Zamfara ranar alhamis.
Kakakin sojoji na kasa Brig.gen Sani Usman ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar ranar juma’a.
Usman yace sojojin sun kawar harin da yan fashi ke neman yi ga al’ummar yankin.
Yace yan fashi sun kashe wani jam’in hukumar FRSC kafin zuwan sojoji.
Usman yace sojojin sun gano bindigar
AK-47 guda biyu da kunshin harsashin bindiga 6 da kuma babura 7 daga yan fashin.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Sojoji sun kashe wani dan fashi, an gano bidigar AK 47 guda 2"

Post a Comment