Hadiza Gabon Ta Zagi Wani Mutumi Saboda Yabata Shawara Tayi Aure

Fitacciyar yar wasan Hausa, Hadiza Gabon ta mayar ma wani abokinta a shafin Twiter amsa cikin bacin rai yayin da ya bata shawarar lokaci yayi da ya kamata ta fitar da miji.
Jaridar Daily Trust ta Mutumin mai suna M.Bash yana baiwa Hadiza Gabon shawara yayin dayake tsokaci a wani sabon hoto da Hadizan ta daura a twitter, inda yace mata “Masha Allah an girma, ai ya kamata a fidda miji”
Jin wannan ya bata ma Hadiza Gabon rai, inda ta amsa da cewa “Toh ko zaka bawa tsoho shawaran ya ma tsohuwa retire ya kawo ni ne?” kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.
Ga dai yadda takaddamar ta kasance:
M.Bash @muhammadbinbas1 Replying to @AdizatouGabon “Masha Allah an girma ai ya kamata a fidda mijin #AURE”
Hadiza AliyuVerified account @AdizatouGabon Hadiza Aliyu Retweeted M.Bash
“Toh ko zaka bawa tsoho shawaran ya ma tsohuwa retire ya kawo ni ne?”
Sakamakon takaddamar data barke, sai jama’a suka shiga tsakani, inda wani mai sunaSkenxy slux @Auwalmesalati ya amsa da cewa “Pls adinga danne xuciya, i dont think parent has anything to do with this sis, beside aure ba farilla bace sunnah ce, badole bane.”

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Hadiza Gabon Ta Zagi Wani Mutumi Saboda Yabata Shawara Tayi Aure"

Post a Comment