Kundin tarihin abubuwan bajinta na Duniya: Matar da tafi kowa farata masu tsawo a Duniya

Wannan hoton wata baiwar Allahce me suna Ayanna Williams dake jihar Texas kasar Amurka wadda ta samu shiga kundin tarihin abubuwan bajinta na Duniya wato Guinness World Record a matsayin wadda tafi kowa farcen hannu me tsawo a Duniya, matar wada dama aikinta shine gyarawa mutane kumba tace ta kwashe shekaru 23 tana tattalin wannan kumbunan nata domin ganin cewa ta samu wannan matsayi.
Tsawon gaba dayan kumbunan nata idan aka hadasu guri daya yakai kafa goma shatakwas sannan tsawon kowanne kumba na yatsa daya yakai kusan kafa biyu, matar tace a kullun tana amfani da sabulu me maganin cututtuka da burushin wanke farata wajen tsaftace faratan nata kuma ta bayyana cewa abinda tafi shan wahalar yi da wadannan farata nata zaro-zaro shine saka wando kuma takan dauki tsawon sati guda kamin tana yiwa faratannata kwalliya.

Matar tace wata abokiyartace ta fara bata shawarar tayi hakan kuma daga nan taji cewa tana son shiga kundin tarihin Duniya dan haka ta dukufa wajan kula da faratan nata har suka kai tsawon haka, tace tana alfahari da kasancewarta cikin wanna kundi. Ayanna Williams dai ta samu shiga kundin bugun shekarar 2018.
Ita kuma wata baiwar Allah daga kasar China ta shiga kundin tarihin abubuwan bajinta na Duniyarne a matsayin wadda tafi kowa tsawon gashin saman ido, matar me suna Jianxia of Changzhou itama tayi alfahari da samun shiga wannan kundin.
Sai kuma mutumin da yafi kowa dadewa yana motsa jiki a Duniya, mutumin me suna Jim Arrington ya shafe shekaru saba'in yana aikin motsa jiki kuma yace baida niyyar dakatawa nan kusa domin abin ya riga ya zamar mai jiki. Shima ya shiga kundin abubuwan ban al'ajabi na Duniya.
Ba mutanene kadai ke samun shiga kundin tarihin abubuwan bajinta na Duniya ba harma da dabbobi dan kuwa ga magen da tafi kowace mage tsawon bindi a Duniya itama ta samu shiga wannan kundi.
Magen dama tana da 'yar uwa wadda itama a shekarun baya ta samu shiga kundin tarihin Duniya a matsayin magen da tafi kowace mage tsawo a Duniya.
Sai kuma wasu bayin Allah suma da suka shiga kundin tarihin abubuwan bajintar na Duniya saboda abinda sukayi, su hamsin suka shiga cikin mota kirar Bas me daukar akasara mutum shida kawai.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Kundin tarihin abubuwan bajinta na Duniya: Matar da tafi kowa farata masu tsawo a Duniya"

Post a Comment