Zaben shugaban kasa:Shugaba Buhari ya lika Atiku da kasa a Kaduna

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC ya lika dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da kasa a jihar Kaduna, kamar yanda sakamakon da INEC ta bayyana a jihar ya nuna.
Jami'in INEC kuma me karbar sakamakon zabe a jihar, Professor Bello B. Shehu ya bayyana cewa, shugaba Buhari ya samu kuri'u 993,482, yayin da shi kuma Atiku Abubakar ya samu kuri'u 613,318, kamar yanda The Nation ta ruwaito.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Zaben shugaban kasa:Shugaba Buhari ya lika Atiku da kasa a Kaduna"

Post a Comment