IS ta kai munanan hare-hare a birnin Bagadaza

Fararen hula takwas ne aka hallaka, yayin da
wasu karin biyar suka samu raunuka a wani
harin kunar-bakin-wake a kudu maso yammacin
birnin Bagadaza na kasar Iraqi.
'Yan harin kunar-bakin-waken sun shiga garin Ain
Tamr, daga yammacin lardin Anbar da sanyin
safiyar Litinin, amma sun gamu da turjiya daga
jami'an tsaro.
An bindige biyar daga cikin maharan, amma
shida sun kutsa cikin wani gida inda suka
tarwatsa kansu tare da hallaka fararen hula.
Kungiyar da ke kiran kanta Kasar Musulunci
wato, IS ta ce ita ke da alhakin kai harin.
A ranar Lahadi ta kaddamar da jerin hare-haren
bama-bamai a ciki da wajen birnin Bagadaza,
abin da ya hallaka akalla mutane 23, tare da
jikkata wasu 70.
Mahukunta sun ce 'yan harin kunar-bakin-waken
da suka kai hari a garin na Ain Tamr, sun sha
yunkurin kutsawa birnin Karbala, inda 'yan Shi'a
ke da rinjaye, mai tazarar kilomita 50 daga
gabashin kasar.
Miliyoyin 'yan Shi'a ne ke yin tattaki zuwa birnin
Karbala don yin bikin kawo karshen makokin
kwanaki 40 na Limamin Shi'a na uku Hussein.
Za a gudanar da bikin na wannan shekarar a
ranar Lahadi.
Hussein, jikan Annabi Muhammad ( SAW) ne,
kuma an hallaka shi a yakin Karbala ne, a cikin
karni na bakwai, a ranar da ake kira Ashura.
Sai dai 'yan Sunni masu tsattsauran ra'ayi na
daukar 'yan Shi'a a matsayin masu sabo, da
hukuncin kisa ya hau kansu, saboda a cewarsu
suna amfani da sunayen iyalan manzon Allah
wajen saba wa dokokin addinin Musuluci.
Kungiyar IS ta sha kai hare-hare a kasar Iraqi tun
bayan da dakarun gwamnati suka kai wani
babban farmakin kwato birnin Mosul da ke
arewacin kasar, daga hannun mayakan.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "IS ta kai munanan hare-hare a birnin Bagadaza"

Post a Comment